Hukumar Kwallon Kafar Premier League Ta Tabbatar da Sababbin Dokoki Domin Kakar Wasa Ta 2026/2027.

Hukumar Kwallon Kafar Premier League Ta Tabbatar da Sababbin Dokoki Domin Kakar Wasa Ta 2026/2027.  

Sababbin Dokokin da Hukumar Ta Premier League Ta Gabatar Sun Haɗa da:
⦿ 'Yan wasan da suka ji rauni ana tsaka da wasan, yanzu dole ne su zauna a wajen fili na tsawon aƙalla minti 1, maimakon daƙiƙa 30 da ake yi a baya.

⦿ Za a ƙirga daƙiƙa 5 wajen jefa ƙwallo (throw-in) da kuma bugun sa wasa (goal-kick), za a miƙa damar fitar da ƙwallon ga ƙunguyar abokan hamayyarsu, idan aka samu jinkiri.

⦿ 'Yan wasan da aka sauya suna da daƙiƙa 10 kacal su fice daga filin, idan ba haka ba wanda zai canje su zai jira har sai an sake tsayar da wasa sannan ya shiga filin.

⦿ Za a iya sake kallon VAR domin gyara kuskuren da aka yi wajen bayar da katin gargaɗi na biyu (yellow card) a fili wanda ke haifar da jan kati.

⦿ Akwai buƙatar masu horaswa su zaɓi ɗan wasan da yake a cikin fili wanda zai fita daga filin wasan na tsawon minti ɗaya, duk lokacin da aka tsayar da wasa saboda raunin mai tsaron raga.

Post a Comment

Previous Post Next Post