Shugaba Bola Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Ɗan’zumi, gwarzuwar ɗiya daga Jihar Gombe kuma 'yar Najeriya abin alfahari, murnar samun nasara a rukunin mata a Gasar Karatun Al-Qur'ani Mai Tsarki Ta Ƙasa da Ƙasa Ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Masarautar Saudiyya.
Wata sanarwa da Babban mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar, ta yabi Maryam saboda bajinta da ƙwarewa ta musamman wajen hardace Alƙur'ani mai tsarki a gagarumar gasar ta ƙasa da ƙasa da aka gudanar a birni mai tsarki na Makka.
Sanarwar ta bayyana cewa ta doke sauran masu gasa daga ƙasashe 132, inda ta samu kyautar Riyal na Saudiiyya 300,000, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 120.
Sanarwar ta ƙara da cewa nasarar da Maryam ta samu, gagarumar nasara ce ba ga kanta kawai ba, a'a, abin alfahari ne ga ƙasa bakiɗaya, kasancewar ta ɗaga sunan Nijeriya a matakin duniya ta hanyar ƙwarewarta a kan Alƙur'ani Mai Tsarki.
Shugaba Tinubu ya bayyana Maryam da yayarta, Hajara Ibrahim Ɗan'azumi, wadda ita ma ta zo ta ɗaya a makamanciyar gasar a ƙasar Urdun (Jordan) a shekarar 2024, a matsayin abin koyi da ƙwarin gwiwa ga matasan Nijeriya.
Shugaban ƙasar ya kuma yabi iyayensu, malamansu, masu horar da su, da duk waɗanda suka ba da gudummawa wajen ci gabansu da nasararsu, yana sane da irin sadaukarwa da jajircewar da ake buƙata don kaiwa ga irin wannan gagarumin matsayi na ilimin Alƙur'ani.
Shugaba Tinubu ya kuma miƙa godiyarsa ga masu shiryawa da hukumomin Masarautar Saudiyya saboda samar da wannan kyakkyawan dandalin ƙasa da ƙasa da ke haɓaka ƙwarewa wajen harda, karatu, fahimta, da ilimin Alƙur'ani.
Nasarar da Maryam Ibrahim Ɗan'azumi ta samu a rukunin da aka yi gagarumar gasa a kai, wanda ya ƙunshi hardar dukkan Alƙur'ani da, ƙira'a da tajwidi da kuma tafsirin dukkan Hizbi 60, wata gagarumar nasara ce da ta kawo babbar karramawa ga Nijeriya, tare da ƙara nuna ƙwarewa da horo da sadaukarwa da kuma zurfin basira.