Arsenal Ta Lallasa Coventry da Ci 3 da Nema 0, a Wasan Farko na Gasar Premier League

A wasan farko na gasar cin kofin Premier League da ake yi a Ingila na kakar wasannin shekarar 2026/2027 masu riƙe da kambun Arsenal ta lallasa Coventry.

Daga ƙarshe dai Arsenal ta tafi da ladar maki uku ringis bayan da ta loda wa Coventry dakon ƙwallaye 3 da nema 0 a raga.

Kai Hervertz ne mutum na farko da ya fara zura ƙwallo a kakar wasan bana 2026/2027 a gasar Premier League, sai Saka da ya ci ƙwallo ta 2 yayin da Martini Ordegard ya zura ƙwallo ta 3 a raga.

Ya zuwa Yanzu giwa ta riga da ta ɗare saman teburin Premier League da maki 3 da kuma ƙwallaye 3.

Shin kuna ganin bana ma Arsenal ce za ta ci gaba da jan ragamar Premier League kamar yadda ta yi a kakar da ta gabata. Ko kuna ganin akwai ƙunguyar da za ta take mata bakin faranti?

Post a Comment

Previous Post Next Post