Kamfanin TikTok da mahaifinsa, ByteDance, sun amince da biyan dala miliyan 400 domin sasanta ƙarar da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta shigar a kansu, bisa zargin cewa manhajar ta karya dokokin tarayya da suka shafi kare sirrin yara, in ji ma’aikatar a ranar Juma’a."66
Ma’aikatar ta ce a cikin yarjejeniyar, TikTok zai biya dala miliyan 300 nan take, sannan ya biya ƙarin dala miliyan 100 bayan kotu ta soke wata tsohuwar yarjejeniyar hukunci da aka sanya wa kamfanin Musical.ly, wanda ya kasance magabacin TikTok.
Ma’aikatar ta bayyana cewa wannan na daga cikin manyan kuɗaɗen da aka taɓa karɓa daga shari’ar da ta shafi dokar kare sirrin yara ta intanet, wato COPPA.
Dokar COPPA ta haramta wa shafukan intanet tattara bayanan sirri na yara ‘yan ƙasa da shekara 13 ba tare da izinin iyayensu ba.
A shekarar 2024, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka da Hukumar Ciniki ta Tarayya (FTC) sun shigar da ƙara kan TikTok, suna zargin manhajar da jefa lafiyar miliyoyin yara cikin haɗari ta hanyar tattara bayanansu ba tare da izinin iyayensu ba.
Hukumomin sun kuma zargi TikTok da bai wa yara damar amfani da manhajar, tare da tattara da amfani da bayanan sirrinsu ba tare da sanar da iyayensu ba.
Ƙarar ta ce hatta asusun da aka ƙirƙira a cikin “Kids Mode”, wanda aka tsara domin masu amfani da shekarunsu bai kai 13 ba, na tattara adireshin imel da wasu bayanan sirri.
A shekarar 2019, Amurka ta shigar da ƙara kan wani manhajar mai suna Musical.ly bisa dokar COPPA. Kamfanin ByteDance ya sayi Musical.ly a shekarar 2017, daga bisani ya haɗa ta da TikTok.
Har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, TikTok bai mayar da martani ga buƙatar jin ta bakinsa kan yarjejeniyar ba.