Tafkin shi ne tafki na biyu da aka samu a saman wani dutse, a duk fadin duniya, ɗayan tafkin shi ne Hanging a Colorado, a kasar Amurka.
Tafkin Iyake daya ne daga cikin abubuwan al'ajabi bakwai na Najeriya. Akwai Jita-jitar cewa tafkin ba shi da karshe a zurfinsa, kuma yana haɗiye duk wanda ya yi ƙoƙari yaga zurfinsa. Kuma an camfa cewa da akwai wata duniya da wata Uwargijiya ke mulki a ƙarƙashin tafkin.
Tafkin Iyake, wanda ke cikin kewayen kauyen Iyake da ke kusa da Ado-Awaye a jihar Oyo, Najeriya, wani abin al'ajabi ne da ke daukar hankali. Wannan tafki mai ban sha'awa yana cikin shimfidar wurare masu ban sha'awa na tsaunuka masu koriyar ciyawa, wannan tafki na musamman ya shahara saboda mahimmancinsa a yanayin ƙasa.
Wannan tafkin ba ya bushewa ko da lokacin rani, kuma ruwansa ya kasance iri daya ne ko a lokacin damina. Bayan tafkin, dutsen yana da wasu abubuwan al'ajabi waɗanda suka mai da shi wuri mai ban sha'awa da al'adun gargajiya.
Tarihi
Yan gudun hijirar Dihormy ne suka gano tafkin Iyake a shekara ta 1500 AD. 'Yan gudun hijirar Dihormy wadanda a yanzu su ne shugabanni masu rike da sarautar Alado na Ado Awaye. Akwai tatsuniyoyi da ke kewaye da tafkin Iyake (Suspended Lake) da kuma dutsen Ado Awaye: “Daya daga cikin tatsuniyoyi shi ne, tafkin Iyake, wata mace ce wacce ba ta taba haihuwa ba, ta koma ruwa kuma take mulki a wata duniya a karkashin ruwan. An kuma yi imanin cewa idan kuna da matsalolin Aljanu ko neman haihuwa ku roki ruwan tafkin yana bada mafita.
Wani Jagoran masu yawon bude ido ya ce tafkin ba shi da karshe a zurfinsa kuma ba a yarda kowa ya yi iyo ko shiga cikinsa ba, domin a tarihi duk wanda yayi iyo a cikin sa ba zai rayu ba.
Dutsen Ado Awaye ya zama gado da cibiyar haɗin kai ga kowa da kowa. Jama'a na bikin Oodua a wurin duk shekara.
Tafiya daga Ibadan zuwa tsaunin Ado kusan mintuna 90 ne a mota. Dole ne ku hau kan tsauni Ado Hill don isa tafkin (tafiyar minti 25).
