Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Rabiu Kwankwaso ya soki lamirin jerin sunayen da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta fitar na waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu a 2027.
A ranar Asabar ne aka fitar da jerin sunayen, inda tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari zai kasance shugaba, sai dai lamarin ya janyo muhawara a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Rabiu Kwankwaso ya ce jerin sunayen “abin damuwa ne ga mutanen Najeriya waɗanda ke cikin wahala a faɗin ƙasar”.
Kwankwaso ya yi zargin cewa akwai matuƙar damuwa game da mutanen da aka sanya a jerin kasancewar an yi amfani da wasu shugabannin hukumomin gwamnati, kamar shugaban hukumar tara kauɗaɗen shiga ta ƙasar, Dr Zacch Adedeji da shugaban ofishin kasafin kuɗi na tarayya Tanimu Kurfi .
Ya bayyana cewa “shugabancin muhimman hukumomin gwamnati na buƙatar mutane waɗanda ba su ɗaukar ɓangare, waɗanda kuma al’umma suka yarda da su.
“Ina kira ga Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya amince ya jagoranci tawagar yaƙin neman zaɓen, ya yi nazari sannan ya sauya tunani,” a cewar Kwankwaso.