Wani Matashi Dan Kungiyar ISWAP Ya Mika Wuya Ga Sojoji a Borno

Wani matashi mai shekaru 25 da ake zargin ya kasance mayakin kungiyar ISWAP, Ali Gambo Kanuri, ya mika wuya ga dakarun soji a Monguno, Jihar Borno kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Ali Gambo Kanuri

Rahotanni sun ce Gambo, dan asalin kauyen Ngarinna a karamar hukumar Monguno, ya shafe kimanin watanni takwas yana cikin kungiyar bayan wani abokinsa ya shigar da shi.

Sai dai daga bisani ya ce ya gaji da rayuwar kungiyar tare da yanke shawarar barin ta, musamman sakamakon matsin lambar da hare-haren sojoji ke yi kan sansanonin ‘yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabas.

Bayan ya tsere daga yankin da kungiyar ke iko da shi, Gambo ya mika kansa ga sojoji a garin Monguno, inda aka tsare shi tare da mika shi ga hukumomin da abin ya shafa domin gudanar da bincike da sauran matakan da suka dace.

Rahoton ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyukan kawar da Boko Haram da ISWAP a sassan Jihar Borno, yayin da hukumomi ke karfafa gwiwar wadanda ke son barin kungiyoyin ta’addanci su mika wuya cikin lumana domin tantancewa da shirin gyara rayuwarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post