INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnan Jihar Osun na daukacin ƙananan hukumomi 30 na jihar.
Bisa sakamakon da hukumar zaɓen ta sanar, ɗan takarar jam’iyyar Accord kuma gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, ya samu ƙuri’u dubu 511,067, inda ya doke babban abokin karawarsa, ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u dubu 444,815.
Ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, shi ya zo na uku da tazarar kuri’u mai yawa, inda ya samu kuri’u dubu 17,180.
Sakamakon da INEC ta bayyana ya nuna cewa Adeleke ya yi nasara a ƙananan hukumomi da dama, ciki har da Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Osogbo, Ife ta Gabas, Ife ta Kudu, Egbedore, Oriade, Odo Otin da Ila.
Oyebamiji kuwa ya samu nasara a wasu muhimman ƙananan hukumomi, ciki har da Irewole, Ife ta Kudu, Isokan, Atakunmosa ta Gabas, Obokun, Ilesa ta Gabas, Boripe da Olorunda.
Bisa jimillar sakamakon da aka gabatar yayin tattara sakamakon zaben na INEC, Adeleke ya samu tazarar kuri’u 66,252 a kan Oyebamiji.
