Bola Ahmad Tinubu ya hori hukumar shirya zaɓe ta ƙas (INEC) da ta yi gaskiya da adalci a zaɓen gwamnan Osun
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci INEC da hukumomin tsaro su tabbatar da cewa zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar a gobe Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026, ya kasance zaɓe cikin lumana, gaskiya da adalci.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana cewa, Tinubu ya ce INEC na da alhakin tabbatar da sahihancin tsarin zaɓen da kuma kare amincin sakamakonsa.
Shugaban ƙasar ya kuma ce yana son INEC ta yi amfani da zaɓen Osun a matsayin gwaji wanda zai nuna shirinta na gudanar da sahihin babban zaɓen 2027 mai zuwa cikin inganci.
Haka nan, ya yi umarni ga rundunar ’Yansandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro waɗanda aka tura jihar ta Osun da su tabbatar da tsaron al'umma masu kaɗa ƙuri’u da kuma jami’an zaɓe, tare da hana kowane mai yunƙurin tayar da hankali ko ƙoƙarin kawo cikas wajen gudanar da zaɓen.
Shugaban kasa ya ƙarfafa wa al’ummar Osun gwiwa da su fito su kaɗa ƙuri’unsu cikin kwanciyar hankali, ba tare da tsoro ko barazana ba.
Ya kuma jaddada cewa sakamakon zaɓen da za a yi na goben, dole ne ya kasance abin da ya dace da zaɓin al’ummar jihar Osun, yana mai cewa sahihancin zaɓen zai dogara ne kan yadda sakamakonsa zai nuna muradin masu kaɗa ƙuri’a.