Jami'an 'yansandan ƙasar Ecuador sun tabbatar da kama hodar Iblis maƙare a cikin wata mota, mai nauyin kilogiram 369 wadda take ɗauke da hoton Haaland a ƙasar Ecuador
Jami'an ‘yansandan sun kama kilogiram 369 na hodar iblis (cocaine) a saƙe a cikin wata mota daura da iyakar ƙasar Colombia, inda aka ci karo da hoton shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Norway wanda yake taka leda a ƙungiyar Manchester City da ke Ingila wato Erling Haaland, a jikin ƙunshi-ƙunshi na hodar iblis ɗin.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yansanda masu yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyin sun dakatar da motar ne bayan da suka samu wasu bayanan sirri, inda suka gano ƙunshi-ƙunshi har guda ɗari uku da saba'in (370) na hodar iblis da aka ɓoye a wani ɓangare na motar mai siffar ƙurƙura.
'Yansandan sun kama direban motar, tare da wata mata mai suna María R., wadda ke ɗauke da takardun shaidar zama ‘yar ƙasar Colombia.
Sai dai kawo lokacin rubuta wannan rahoton jami'an ‘yansandan ba su bayyana dalilin amfani da hoton Haaland a jikin ƙunshin hodar iblis ɗin ba. Sai dai rahotanni sun ce masu safarar miyagun ƙwayoyi kan yi amfani da sunaye ko hotunan fitattun ‘yan wasa da mashahuran mutane wajen tantance ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyin da kuma kwastomominsu.
A wasu rahotannin kuma, an ce hoton kyaftin ɗin Inter Miami ɗan ƙasar Argentina, Lionel Messi, ya taɓa bayyana a kan wasu ƙunshin miyagun ƙwayoyi da aka kama.
Daga ƙarshe an ƙiyasta adadin kuɗin hodar iblis ɗin da aka kama wanda ya kai kusan darajar dala miliyan 11 a Amurka, yayin da darajarsa ta haura dala miliyan 19.6 a Turai.
Ya zuwa yanzu, 'yansandan ƙasar Ecuador sun ce sun kama kusan tan 80 na miyagun ƙwayoyi a farkon rabin shekarar 2026, idan aka kwatanta da kusan tan 215 da aka kama a shekarar 2025.