Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce Boko Haram ta lalata gine-ginen makarantu aƙalla 5,000, lamarin da ya sa yara miliyan 2.2 ba sa zuwa makaranta a lokacin da rikicin ta'addanci ya yi ƙamari.
Kakakin gwamnan, Malam Dauda Iliya, ya shaida wa BBC cewa gwamna Zulum ya duƙufa wajen ganin an shawo kan matsalar tsaron tare da inganta fannin ilimi ganin irin girman ɓarnar da Boko Haram ta yi wa ɓangaren.
A cewar kakakin, gwamnan ya gina azuzuwa kusan 5000 da gina wasu makarantu 129 sannan kuma ana sa ran kammala wasu 140 daga nan zuwa ƙarshen mulkinsa.
Ya ce akwai yara sama da miliyan ɗaya da dubu 800 da suke makaranta saɓanin lokacin da gwamna Zulum ya karɓi mulki inda a lokacin yara dubu 800 ne kaɗai suke zuwa makaranta.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa Boko Haram ta kashe malamai da jami'an kula da makarantu da dama musamman a lokacin da yaƙin ya yi ƙamari.
Zulum ya ce gwamnatinsa ta ware dala miliyan 35 a tsakanin shekarar 2025 da 2026 don inganta ilimin pramare da sakandare.