Shugaban Kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya sayi jirgin sama mai nasa na kansa na farko lokacin da yake da shekara 22 da rabi.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin bikin ƙaddamar da sayar da hannun jarin matatar mai ta Dangote ga jama’a.
Da yake waiwayar tafiyar da ya yi a harkar kasuwanci, hamshakin attajirin ya ce ya ji daɗin rayuwarsa ta kasuwanci, amma a yanzu ya fi mayar da hankali wajen amfani da dukiyarsa wajen saka hannun jari a harkokin da za su samar da ci gaba.
Dangote ya ce yanzu ba shi da matsala da yin amfani da jirgin kasuwanci ko wasu hanyoyin sufuri, duk da cewa ya mallaki jirgin sama mai zaman kansa tun yana da shekaru 22 da rabi.
Ya kuma yi kira ga attajiran Najeriya da ke mallakar jiragen sama masu zaman kansu masu tsada da su karkatar da wani ɓangare na dukiyarsu wajen zuba jari a masana'antu da sauran ayyukan da za su amfani tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce Najeriya ba za ta iya cimma cikakken matsayinta na ƙasa mai ƙarfi ba matuƙar ba a ƙara zuba jari a harkokin samar da kayayyaki da sauran ayyukan tattalin arziki ba.
Dangote ya ce yana ƙoƙarin ƙarfafa masu hannu da shuni da ke kashe makudan kuɗaɗe wajen mallakar jiragen sama da su mayar da irin wannan kuɗi wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
