Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Cire Tallafin Man Fetur

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan matakan da ya dauka na cire tallafin man fetur da kuma sassauta tsarin canjin kudaden waje.

Dangote

Dangote ya bayyana hakan ne ranar Litinin a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya da ke Legas, yayin bikin kaddamar da sayar da hannayen kamfanin matatar mai ta Dangote ga jama'a.

Ya ce kamfaninsa zai ci gaba da hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya domin taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar da nahiyar Afirka.

Dangote ya kuma bayyana mamakinsa kan yadda kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu ci gaba, yana mai cewa bai taba tsammanin za ta kai matsayin da take a shekarar 2026 ba.

Kamfanin ya fara sayar da sabbin hannaye biliyan 4.1 na matatar Dangote kan naira 525 kowanne, inda mafi karancin saye ya kasance hannaye 10, kan N5,250.

Za a rufe sayar da hannayen ne a ranar 13 ga Oktoba 2026, bisa sharuddan yarjejeniyar sayarwar.

Post a Comment

Previous Post Next Post