A sabuwar danbarwar da ta kunno kai tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka, ƙasar ta sanar da taƙaita ba da Visa ga mutanen da ake zargi da nuna wariya ko kin jinin tsirarun farar fata ƴan Afirka ta Kudu.A sabuwar danbarwar da ta kunne kai tsakanin Afurka ta Kudu da Amurka, kasar ta sanar da takaita ba da Visa ga mutanen da ake zargi da nuna wariya ko kin jinin tsirarun farar fata ƴan Afurka ta Kudu.
Gwamnatin shugaba Trump ta soki batutuwa da dama da suka hada da tsarin Afurka ta Kudu na magance wariyar launin fata da ƙyamar ƴan kasashen waje musamman ƴan asalin Poland da Faransa da ke zaune a ƙasar.
Sai dai Afurka ta Kudu ta musanta zarge-zargen, inda ministan harkokin wajen ƙasar Ronald Lamola ya ce su na nazari akai.
Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya jaddada cewa hukumomin Afurka ta Kudu ba su taɓuka abin azo a gani ba don shawo kan matsalar.