A karon farko kafar yada labaran Amurka ta CBS kuma abokiyar hular BBC, ta wallafa hotunan abin da ta kira girman ɓarnar da hare-haren Iran suka yi wa sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
CBS ta ce hare-haren sun yi mummunar ɓarna, inda gine-gine suka rushe da lalata motocin sojoji da sauran abubuwa masu muhimmanci sakamakon harin jirage marassa matuƙa da Iran ta kai.CBS ta ambato ɗaya daga cikin sojojin da aka girke a wurin na cewa, ba a bayyana wa Amurkawa girman ɓarnar da hare-haren suka yi ba.
"An yi wa sansanonin Amurka gagarumar ɓarna, amma an lulluɓe batun ba a son bayyanawa. Mu na fuskabtar hare-hare babu ƙaƙƙautawa, kuma ba mu da ikon mai da martani," in ji shi.
Cikin hotunan da aka yaɗa akwai wanda a ka yi zargin an ɗauke shi ne a sansanin sojin sama na Prince Sultan da ke Saudiyya. Hoton ya nuna abin da a ka yi amanna da cewa lalacewar da sansanin ya yi ne bayan kai harin kan jirgin yaƙi samfurin Boeing A-3 Sentry.
Bayan jirgin ya fita daga jikinsa, yayin da sauran ɓangaren ya ƙone.
Gidajen da ke sansanin sun ruguje wasu sun ƙone, yayin da na'urar da ke ankarar da sojoji lamuran da ke faruwa a sararin samaniya ta lalace baki daya.