Amurka ta ce za ta tallafa wa Najeriya da wasu kayan aikin soja, yayin da ƙasashen biyu ke ƙara ƙarfafa haɗin guiwa wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da sauran barazanar tsaro.
Rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afirka (AFRICOM) ta ce wani jirgin sama na rundunar sojin saman Amurka kirar C-17 ne zai kai kayan aikin ga rundunar sojin saman Najeriya a ƙarshen wannan mako.A cewar AFRICOM, kayan aikin wani ɓangare ne na yarjejeniyar sayar da kayayyakin soji tsakanin ƙasashen biyu, wadda ke ƙara ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya, tare da taimakawa ƙoƙarin Najeriya na yaƙi da ta'addanci a yankin.
Isar da kayan aikin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya na masu iƙirarin jihadi da kuma ƴan bindiga da sauran barazanar tsaro.
Kodayake rundunar sojin Najeriya ta samu wasu nasarori a watannin baya-bayan nan, hare-hare da sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba a wurare da dama.
Najeriya da Amurka sun kuma ƙara haɗin gwiwa a fannonin musayar bayanan sirri, horas da jami'an tsaro da kuma ba da tallafin soja.
A watan Janairu ne dakarun Amurka suka kai wasu kayayyakin soja Najeriya, inda suka ce matakin na tallafa wa ayyukan tsaron da ƙasar ke gudanarwa, tare da nuna irin dangantakar tsaro da ke tsakaninsu.
Kimanin sojojin Amurka 200 da aka tura Najeriya a farkon shekarar nan domin wani aikin yaƙi da ta'addanci sun janye bayan kammala aikinsu.
Sai dai haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu na ci gaba.
Daga cikin horon da Amurka ta bayar a baya-bayan nan a Najeriya akwai yadda ake sarrafa jirage marasa matuƙa, dabarun yaƙi da abubuwan fashewa da kuma kula da waɗanda suka jikkata a filin daga.