Kotun Daukaka Kara Ta Amurka Ta Yi Watsi Da Bukatar Trump Kan Sabbin Dokokin Zaben Wasiku

 Wata kotun ɗaukaka ƙara ta Amurka ta ƙi amincewa da buƙatar gwamnatin Shugaba Donald Trump na aiwatar da sabbin dokoki da za su tsaurara ƙa'idojin zaɓe ta hanyar wasiƙu (mail-in voting) kafin zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar na 2026.

Donald Trump

Kotun ta tabbatar da wani hukuncin da ƙaramar kotu ta yanke na dakatar da aiwatar da sabbin ƙa'idojin. Waɗannan dokoki sun shafi yadda Jihohi za su tsara da kuma tura takardun zaɓe ta hanyar hukumar gidan waya ta Amurka.

Masu kare haƙƙin masu zaɓe da wasu Jihohin da Democrats ke jagoranta sun yi adawa da dokokin, suna cewa za su iya hana mutane da dama damar kaɗa ƙuri'a. Sai dai gwamnatin Trump ta ce matakan suna da nufin inganta tsaro da sahihancin zaɓe.

Batun yanzu na gaban Kotun Ƙolin Amurka, wadda ake sa ran za ta yanke hukunci kan makomar waɗannan ƙa'idoji. Hukuncin zai iya yin tasiri sosai kan yadda za a gudanar da zaɓen rabin wa'adin majalisar dokokin Amurka na 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post