Harin Iran a Jordan ya Lalata Jiragen Yakin Amurka 20

Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti da ke Jordan da safiyar Laraba.

Tashar labarai ta CBS News ta Amurka, abokiyar hulɗar BBC, ta ruwaito cewa harin ya yi sanadin lalacewar wasu jiragen yaƙin sojin Amurka da ke sansanin.

Rahotanni sun nuna cewa kusan jiragen yaƙi kirar F-15 guda takwas sun samu ƙananan matsaloli sakamakon harin.

Majiyoyi sun ce bayan an gyara jiragen, an mayar da su aiki cikin rundunar sojin saman Amurka.

Haka kuma, majiyoyin sun ce wani jirgin yaƙi kirar A-10 Thunderbolt, wanda aka fi sani da "Warthog", ya yi matukar lalacewa bayan makami mai linzami ya faɗa masa, lamarin da ya lalata ɗaya daga cikin fika-fikansa gaba ɗaya.

Wata majiya daga ɓangaren leƙen asiri da ta tattauna da CBS News ta ce babu wani sojan Amurka da ya rasa ransa a harin.

Sai dai saboda muhimmancin lamarin, majiyoyin sun buƙaci a sakaya sunayensu.

Rahoton ya kuma ce dakarun Amurka da ke Jordan sun harba sama da makamai masu linzami na kariya kirar Patriot guda 30 a matsayin martani ga harin na Iran.

Kafin wannan hari, Amurka ta bayyana cewa ta kai hare-hare kan tankokin jigilar man fetur na Iran guda biyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post