Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya musanta rahotannin cewa ya ƙi tayin zama mataimakin Atiku Abubakar, wanda yake takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, a zaɓen 2027 mai zuwa.
Peter Obi ya bayyana hakan ne, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV, inda yake magana kan yiwuwar haɗakar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Obi ya ce babu wani tayin da aka yi masa na zama mataimakin Atiku da ya ƙi amincewa da shi, ya kuma ƙara da cewa, a lokacin da ake magana kan batun, bai ma kasance cikin yanayin da za a yi masa irin wannan tayin ba.
“Ban san inda aka faɗi hakan ba. Ban ma kasance a matsayin da ake yi min tayin ba, balle in ƙi,” in ji Obi.
A shekarar 2025, Obi da Atiku da wasu shugabannin adawa sun kafa ƙawance ƙarƙashin jam’iyyar ADC. Sai dai daga baya ƙawancen ya samu tangarɗa, inda wasu daga cikin mambobinsa suka fice daga haɗakar, yayin da Obi ya zama ɗan takarar NDC, Atiku kuma ya zama ɗan takarar ADC.
Da aka tambaye shi ko zai janye wa Atiku ko kuma ya amince da kujerar mataimakin shugaban ƙasa idan aka cim ma yarjejeniyar haɗaka, Obi ya ce batun ya wuce tsakanin mutane biyu.
Ya ce duk wata yarjejeniya ta haɗakar jam’iyyun adawa dole ta kasance tsakanin jam’iyyun, ba wai tsakanin ’yan takara kaɗai ba.
Obi ya ƙara da cewa, zai goyi bayan duk wata ƙawance da za ta mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa, bin doka da shugabanci na gaskiya da riƙon amana da inganta ilimi da kiwon lafiya da samar da ayyukan yi da kuma rage talauci a cikin ƙasa.
Idan ba mu manta ba, Peter Obi da Atiku sun taɓa yin takara tare a zaɓen shugaban ƙasa na 2019, inda Obi ya kasance mataimakin Atiku a lokacin. Sai dai a zaɓen 2023 sun tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban, Obi a ƙarƙashin Labour Party (LP) yayin da Atiku kuma ya tsaya takara a ƙarƙashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).