Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙarɓi ragamar Sabuwar Cibiyar Kirƙire-Kirƙire da Fasaha ta Samari da 'Yan Mata (Adolescent and Young People Innovation Tech Hub) biyo bayan miƙa ta a hukumance da Cibiyar IHVN ta yi.
Wannan cibiya ta mai ɗauke da ɗakuna 12 waɗanda aka ƙawata da na'urorin zamani, za ta samar da damarmaki a fannoni daban-daban da suka haɗa da: fasahar sadarwa (ICT) da ƙirar yanar gizo da ƙirƙirar abubuwan yanar gizo da fasahar kwalliya da kasuwanci, da horar da sana'o'i, tare da samar da tallafin lafiya da jin ƙai ga matasa.
Wannan shiri ya yi daidai da Tsarin Gina Makoma (Building Your Future Agenda) na gwamnatin jihar, musamman wajen haɓaka ilimin ɗan adam da tallafa wa matasa. Tuni dai sama da matasa 1,200 suka amfana da shirye-shirye daban-daban a Cibiyar Sana'o'in Matasa Ta Katsina.
Muna miƙa godiya ga Cibiyar CDC ta Amurka da IHVN saboda tallafin kuɗi da fasaha da suka bayar domin tabbatar da wannan aiki.