Kabilar Kuraishawa Da Tasirinta A Cikin Larabawa

Kabilar kuraishawa ita ce mafi daukakar kabila kuma mafi daraja daga cikin kabilun larabawa. Kuma ana danganta sunan wannan kabila ne da kakan manzon ALLAH (SAW) na goma mai suna kuraishu wanda aka fi sani da fihir dan malik. Kuma duk balaraben da nasabarsa ba ta biyo ta fihir dan malik ba to ba bakuraishe ba ne.

Larabawa

Kabilar Kuraishawa ta taka muhimmiyar rawa a tarihin rayuwar Annabi Muhammad (SAW) saboda ita ce kabilar da ta ke jagorancin al'ummar Makka kafin zuwan Musulunci.

Sura ta dari da shida a cikin Alkur’ani mai girma ana kiranta da “Kuraish”. An sanya wannan sura a cikin sura ta talatin da ayoyi 4. “Kuraish”, wacce surar Makka ce, ita ce sura ta ashirin da tara da aka saukar wa Annabi Muhammad (SAW).

Da yawa daga malaman tafsirin kur’ani mai tsarki sun dauki wannan sura a matsayin ci gaban surar “Giwaye”. Suratul fil, tana magana ne akan barazanar makiya da kokarinsu na rusa Ka'aba, amma a cikin wannan sura an ambaci zaman lafiya da kabilar Kuraishawa ta samu a Makka.

Post a Comment

Previous Post Next Post