Trump Ya Bukaci Zelenskyy Ya Dakatar da Hare-hare Kan Rasha


Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Lahadi ya bukaci Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, da ya dakatar da hare-haren da sojojin Ukraine ke kai wa wuraren tace da samar da man dizal a Rasha, yana mai cewa hare-haren na haddasa ƙarancin man fetur.

Wani ɗan jarida ya tambayi Trump ko ya yi magana da Zelenskyy bayan tattaunawar da ya yi kwanan nan da Shugaban Rasha, Vladimir Putin. Trump ya mayar da martani da kiran Zelenskyy da ya dakatar da kai hare-hare kan Rasha.

“Abu guda ne Mista Zelenskyy ya kamata ya yi,” Trump ya shaida wa manema labarai yayin ziyararsa a Ireland. “Dole ne ya daina lalata wuraren samar da man dizal a Rasha.”

Trump ya ce Ukraine na iya ci gaba da kai hare-hare kan wasu wuraren da take ganin sun dace, amma bai kamata ta kai hari kan wuraren man dizal ba, saboda hakan na ƙara haddasa ƙarancin man.

“Ya ci gaba da kai hari kan wasu wurare, amma ba wuraren man dizal ba, domin yana haddasa ƙarancin dizal,” in ji Trump. “Ba abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya ne ke haifar da wannan ba; abin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine ne.”

Trump ya ƙara da cewa ya tattauna da shugaban Ukraine kan yadda Kyiv ta ƙara yawan hare-haren da take kai wa irin waɗannan wurare a cikin ’yan watannin nan.

Akwai wasu wurare da dama da za a iya kai wa hari. Kada a kai hari kan man dizal, domin hakan na cutarwa. Yana cutar da duniya. Ba ma son ya kai hari kan wuraren man dizal... Yana kai hari kan matatun mai na dizal,” in ji Trump.

Ukraine ta shafe watanni tana kai hare-hare masu nisa kan masana’antar mai da iskar gas ta Rasha. Kyiv ta ce wannan masana’anta na taimaka wa Moscow wajen samun kuɗin da take amfani da shi wajen gudanar da mamayar da ta shafe sama da shekaru huɗu tana yi wa Ukraine, tare da samar da makamashin da ke taimaka wa ayyukan sojinta.

A halin yanzu, Ukraine na harba jirage marasa matuƙa da adadi mafi yawa zuwa cikin Rasha, yayin da Moscow ke mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da suka kai matakin da ba a taɓa gani ba.

A ranar Lahadi, wani jirgin sama mara matuƙa na Rasha ya kai hari kan jirgin ƙasa mai ɗauke da fasinjoji da ke kan hanyarsa daga Kyiv zuwa Warsaw, amma Poland da Ukraine sun ce babu wanda ya jikkata ko ya mutu.

Zelenskyy ya kuma ce an kai hare-hare kan yankunan yammacin Ukraine.

Hare-haren sun faru ne kwanaki kaɗan bayan jami’an Amurka sun kai ziyara Moscow da Kyiv, a wani yunƙuri na Washington na farfaɗo da tattaunawar da za ta iya kawo ƙarshen rikicin da ya zama mafi muni a Turai tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

A gefe guda kuma, sake tsananta rikici a Yammacin Asiya ya sa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya ƙara tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki a Amurka.

Wannan yanayi ya kuma haifar da hasashen cewa Babban Bankin Tarayya na Amurka (Federal Reserve) na iya ƙara yawan kuɗin ruwa, a daidai lokacin da masu zaɓe a Amurka ke shirin kada ƙuri’a a zaɓen tsakiyar wa’adin gwamnati da za a gudanar a watan Nuwamba.

Post a Comment

Previous Post Next Post