A ranar Talata da ta gabata ne, mai magana da yawun Atiku Abubakar ya fitar da wani saƙo da ya soki shirin NELFUND tare da alƙawarin yafe basussukan da aka ƙaƙaba wa ɗalibai da sunan tallafi.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC Atiku Abubakar, ya soki tsarin rancen karatu na NELFUND, wanda shugaban ƙasa Bila Ahmad Tinubu ya fito da shi, bayan ya janye tallafin karatun a ƙasar bakiɗaya, yana mai cewa rance ba tallafin karatu ba ne, bashi ne wanda ɗalibi zai biya daga baya.
Ta bakin mai magana da yawunsa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya bayyana ƙudurin Atiku cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027, ya ɗauki alƙawarin zai rage kuɗaɗen ilimi tare da yafe basussukan ɗaliban da suka cancanta bayan gudanar da cikakken nazari kan tsarin.
Atiku ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙara tsadar ilimi, tare da ƙirƙiro hanyar ba ɗalibai rance domin su iya jure tsadar karatun.
Atiku ya kuma ƙalubalanci gwamnatin Tinubu, tare da neman gwamnatin da ta fitar da bayanan lissafin da yake nuna yadda shirin rage farashin man fetur zai shafi tsarin NELFUND da albashin ma’aikata ko mafi ƙarancin albashi.
Atiku ya ƙara da cewa, manufarsa ita ce rage tsadar rayuwa ta hanyar rage kuɗaɗen makamashi da sufuri, yana mai cewa ilimi bai kamata ya fara da ɗora wa matasa tarin bashi ba.