ICC Ta Dakatar Da Yarjejeniyar Da Kamfanin Inshorar Faransa Kan Barazanar Takunkumin Amurka

 Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta kawo ƙarshen yarjejeniyarta da kamfanin inshorar Faransa AXA, yayin da ake fargabar cewa sabbin takunkuman da Amurka ke shirin ƙaƙabawa kotun na iya jefa kamfanin cikin matsala.

ICC

Yarjejeniyar ta ƙare ne daga 1 ga Oktoba 2026. AXA ce ke ba ma'aikatan ICC inshorar lafiya da rayuwa, kuma kotun ta ce yanzu za ta yi amfani da wani sabon kamfanin inshora, ko da yake ba a bayyana sunan kamfanin ba.

Rahotanni sun ce AXA da ICC sun shafe watanni suna neman hanyar da za ta ba su damar ci gaba da yarjejeniyar ba tare da kamfanin ya fuskanci matsalar takunkumin Amurka ba. Sai dai ba su samu mafita ba, musamman saboda yiwuwar amfani da dokar Turai da ake kira “blocking statute”, wadda ke kare kamfanonin Turai daga wasu tasirin takunkuman ƙasashen waje.

Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta ƙara matsa lamba kan ICC, tana zargin kotun da wuce gona da iri wajen neman ikon hukunta 'yan ƙasashen da ba su amince da dokar kafa kotun ba, ciki har da Amurka da Isra'ila. Amurka ta kuma riga ta kakaba takunkumi na kuɗi da hana wasu jami'an ICC shiga ƙasar.

Matakin ya nuna irin matsin lambar da ICC ke fuskanta daga Amurka, yayin da kotun ke ƙoƙarin rage dogaro da tsarin kuɗi da fasahar Amurka. Sai dai Tarayyar Turai ta sake jaddada goyon bayanta ga aikin ICC.

Post a Comment

Previous Post Next Post