Mafarautan Sun Yi Ajalin Barayin Daji Goma Sha Hudu (14), Tare da Kwato Wasu Mutane 3 Yayin Wata Arangama a Jihar Katsina

Mafarauta a jihar Katsina sun kashe wasu 'yan bindiga 14 da ake zargi da aikata munanan laifuka. Mafarautan sun hallaka ɓarayin dajin ne a yayin da suka yi musayar wuta da su bayan sun kai hari kan matafiya a ƙauyen Gidan Wawo da ke ƙaramar hukumar Bakori.

Duk da haka, arangamar ta yi sanadin mutuwar wani mafarauci mai suna Mohammed Ibrahim Jidda, mai shekaru 29, yayin da Usman Sunday, mai shekaru 25, ya samu raunin harbin bindiga, sannan kuma wani matafiyi shi ma ya rasa ransa a arangamar. Haka kuma, an ceto wasu mutane uku da ɓarayin suka yo garkuwa da su.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Dr Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar.

Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kan wasu ’yan bindiga 26 da ke kan babura 13, waɗanda suka nufi dajin Dawan Laila da ke ƙaramar hukumar Bakori.

Da misalin ƙarfe 1:31 na ranar Juma’a, ’yan bindigar suka kai hari kan matafiya da ke kan hanyarsu daga Kakumi zuwa kasuwar Illela ta jihar Sakkwato. A yayin harin, sun ƙona motar wani mutum mai shekaru 50, Jamilu Lawal tare da shi a ciki, wanda ya ƙone har lahira.

Faruwar wannan lamarin ne ya sa mafarautan Gidan Wawo suka tattara kayansu domin tunkarar maharan, inda suka kashe mutane 14 daga cikinsu.

Gwamnatin jihar ta ce bayanan sirri sun nuna yiwuwar ’yan bindigar za su kai harin ramuwar gayya sakamakon asarar da suka yi.

Gwamnatin ta ƙara da cewa, tana haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin ɗaukar matakan da suka dace don hana sake kai hare-hare. Gwamnatin ta yaba wa mafarautan da jami’an tsaro bisa jajircewarsu, tare da kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu kuma su riƙa kai sahihan bayanai ga jami’an tsaron, domin ganin an kawo ƙarshen wannan matsala.

Post a Comment

Previous Post Next Post