Shugaba Tinubu Ya Zargi 'Yan Adawa a Matsayin Wadanda Suka Haddasa Yunwa da Talauci a Najeriya

Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya zargi ’yan adawarsa da haddasa yunwa da talauci da ake fuskanta a ƙasar, yana mai cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalolin.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees da ke jihar Kaduna, gabanin zaɓen 2027.

“Na ji ’yan adawa na magana kan yunwa da talauci. Wane ne ya haddasa su? Su ne! Su ne suka haddasa yunwa da talauci. Mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su,” in ji Tinubu.

Shugaban ya kuma kare manufofin gwamnatinsa, yana mai cewa ana biyan albashi a kan lokaci, tare da yabawa gwamnonin APC kan ayyukan raya ƙasa da suke gudanarwa.

Tinubu ya gode wa al’ummar jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda ya ce ya taimaka masa wajen samun nasara.

“Kun ba ni farin cikin tunawa da nasarar da kuka ba ni na zama shugaban ƙasa. Na dawo ne domin in sake gode muku,” in ji shi.

Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su sake ba shi dama a zaɓen 2027, yana mai cewa yana son ci gaba da aiwatar da ayyukan da ya faro na ci gaba da bunƙasa ƙasa.

Taron, wanda ya gudana a filin wasa na Ranchers Bees, wanda aka fi sani da Kaduna Township Stadium, ya kasance ƙaddamar da fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC gabanin babban zaɓen 2027.

Manyan shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta daga sassa daban-daban na ƙasar sun halarci taron domin fara tattara goyon bayan sake zaɓen Tinubu.

Post a Comment

Previous Post Next Post