Bincike ya zama ɗaya daga cikin hajar Kamfanin Stanbic IBTC, wanda ke cikin rukunin kamfanonin Standard Bank Group, ya sake jaddada muhimmancin haɗin guiwa, ƙwarewar da ta dace da zamani da kuma samun damar kuɗaɗen gudanar da ayyuka wajen mayar da bincike da kirkire-kirkire a Najeriya zuwa sana’o’i masu inganci da za su iya samar da riba.Kamfanin ya bayyana hakan ne ta hanyar ɗaukar nauyi da kuma halartar taro karo na biyu na fasaha da kirkire-kirkire, wanda Ofishin Ƙasa na Samar da Fasaha da Bunƙasa Fasahohi (NOTAP) ya shirya, mai taken Taron Fasaha da Kirkire-kirkire na Ƙasa (NTIS 2.0).
Taron, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Daga Bincike zuwa Arziki: Ƙarfafa Kirkire-kirkire da Mayar da Bincike zuwa Kasuwanci da Samar da ‘Yancin Kai a Fasaha a Najeriya,” ya haɗa wakilai daga gwamnati, jami’o’i, cibiyoyin bincike, masana’antu da ɓangaren kuɗi domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen fitar da sababbin dabaru daga cibiyoyin bincike zuwa kasuwa.
Da yake tsokaci kan taron, babban jami’in fasahar sadarwa na Stanbic IBTC Holdings, Okechukwu Nwoke, ya ce kirkire-kirkire na iya samar da babbar fa’ida ga tattalin arziki idan aka ba da tallafin da ya dace domin mayar da ingantattun dabaru daga bincike zuwa kasuwa.
Nwoke ya ƙara da cewa, “A Stanbic IBTC, mun yi imanin cewa haɗin guiwa, bunƙasa ƙwarewa da samun damar kuɗaɗe na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen gina sana’o’i masu ɗorewa da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arzikin Najeriya.”
A nasa jawabin yayin wata tattaunawa ta musamman a taron, shugaban sashen fasahar sadarwa na Stanbic IBTC Pension Managers, Ndukwe Anagha, ya bayyana irin damar da Najeriya ke da ita ta fuskar kasuwanci da kuma ƙarfinta na samar da kamfanoni da za su iya gogayya a kasuwannin duniya.
Ndukwe ya jaddada buƙatar ƙarfafa manhajojin karatu a manyan makarantu da kuma samar wa matasan Najeriya ƙwarewar da ta dace da sabbin fasahohin zamani.
Ya bayyana cewa ilimi da ci gaba da koyon sababbin ƙwarewa za su taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin Najeriya na bunƙasa kirkire-kirkire, tare da shirya matasa domin taka rawar gani a tattalin arzikin zamani da fasahar dijital ke ci gaba da sauya fasalinsa.
A wani jawabi da aka gabatar a madadin babban sakatare na ma’aikatar tarayya mai kula da kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Dakta Mukhtar Yawale Muhammed, daraktan kula da saye da daidaita fasahohi, Mista Ampe Fut, ya yi kira da a samar da ingantattun hanyoyin haɗa bincike da masana’antu, masu zuba jari da kuma manufofin ci gaban ƙasa.
Ya ce, “Najeriya ba ta rasa dabaru, hazaka ko ƙarfin gudanar da bincike ba. Babban ƙalubalenmu shi ne yadda za mu samar da tsare-tsare masu inganci da za su haɗa sakamakon bincike da kirkire-kirkire da masana’antu, masu zuba jari, kasuwanni da kuma manufofin ci gaban ƙasa.”
Ita ma da take magana, darakta-janar kuma babbar shugabar NOTAP, Dakta Obiageli Edith Amadiobi, ta bayyana ƙoƙarin hukumar na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da masana’antu.
Ta ce daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke aiwatarwa akwai shirin haɗin gwiwa tsakanin NOTAP da masana’antu domin musayar ƙwarewar fasaha, wanda aka sani da NOTAP-Industry Technology Transfer Fellowship, da kuma wani shiri da aka tsara domin inganta dakunan gwaje-gwaje na bincike.
Ta bayyana cewa shigar kamfanoni cikin tsara abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai wajen gudanar da bincike na iya ƙara yiwuwar mayar da sakamakon binciken zuwa kayayyaki ko ayyukan da za a iya sayarwa a kasuwa.
Ta kuma bayyana tallafin samar da kayayyaki, samun kuɗaɗen gudanar da ayyuka da kuma damar shiga kasuwanni a matsayin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen gina ingantaccen tsarin mayar da bincike zuwa kasuwanci.
Ta hanyar ɗaukar nauyi da halartar NTIS 2.0, Stanbic IBTC ta ba da gudummawa ga tattaunawar da aka gudanar kan haɗin gwiwa, ƙwarewa da hanyoyin samun kuɗaɗen da ake buƙata domin mayar da sabbin dabaru masu amfani zuwa sana’o’i masu ɗorewa.
Shigar kamfanin cikin taron ya kuma nuna yadda rukunin kamfanonin ke ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa bunƙasa sana’o’i, haɓaka ƙwarewar ma’aikata da kuma ci gaban tattalin arzikin Najeriya ta hanyar kirkire-kirkire.