Shugaban Hukumar Zabe, Wa'adi Ya Karato

Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) Farfesa Mahmud Yakubu, a wani taron da ya gudana a watan Afrilu 2025 na shugabannin hukumomin zaɓe na ƙasashen ECOWAS da aka yi a Banjul babban birnin Gambiya, ya bayyana cewa, a watan Disambar 2025 nan ne wa'adin mulkinsa yake cika.
Farfesa Mahmud shi ne shugaban hukumar zaɓe ta ƙasar Nijeriya wanda ya fi daɗewa a kan kujerar tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokuraɗiyya. Ya fara mulki ne tun a wa'adin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari na farko, wanda ya naɗa shi a 9 ga watan Nuwamba 2015, wanda aka naɗa shi domin yin wa'adin shekara 5 kamar yadda doka ta tanada, amma bayan cikar lokacin sai marigayi Buhari ya sake naɗa shi a matsayin shugaban INEC karo na biyu, wanda yanzu yake tunkarar shekara ta goma cifcif a kan kujerar.
Farfesa Mahmud ya gudanar da manyan zaɓuka guda biyu na shekarar 2019, da kuma 2023.
Wa kuke tunanin zai maye gurbin Farfesa Mahmud?

Post a Comment

Previous Post Next Post