Kamar yadda jaridar Mikiya ta ruwaito, fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci gwamnatin jihar Kano da ta saki Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara tare da daina kame-kamen malamai a jihar. Sheikh Gumi ya ce "ya kamata gwamnati ta samar da tsari na baiwa kowa ‘yancin yin wa’azi cikin hikima da lumana, domin gujewa rikice-rikice da hana walwalar addini."
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shafe kusan shekaru huɗu yana tsare a gidan yari tun lokacin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bayan gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW). Sheikh Gumi ya jaddada cewa kawo ƙarshen takurawa malaman addini zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna a Kano da Najeriya baki ɗaya.
