Abubuwa Goma Sha Ɗaya Da Ya Kamata A Sani Game Da Funmilayo Ransom Kuti, Matar Da Ta Fara Tuka Mota A Nijeriya

.Funmilayo Ransom Kuti (Matar Da ta fara tuka mota a Najeriya)

Funmilayo Ransom Kuti ta kasance mace ɗaya tilo a jerin sunayen ‘yan gwagwarmayar neman ‘yancin kan Nijeriya. Fumilayo ta kasance malamar makaranta, ‘yar siyasa, mai fafutukar kare ‘yancin mata sannan kuma mai riƙe da sarautar gargajiya. Ita ce mahaifiya ga shahararren mawakin nan na Nijeriya, Femi Kuti. Funmilayo ce mace ta farko da ta fara tuƙa mota a Nijeriya. An zaɓe ta a majalisar sarakunan gargajiya, inda ta kasance wata wakiliya ta al’ummar Yarabawa. Fafutukar da ta yi ta janyo wa ‘ya’yanta baƙin jini musamman lokacin gwamnatocin soji.

Funmilayo Ransom Kuti

An haifi Fumilayo Ransome Kuti a garin Abeokuta da ke cikin jihar Ogun a yanzu, kuma ita ce ɗaliba ta farko da ta fara shiga makarantar Grammar Abeokuta. Tun tana matashiya, ta yi aiki a matsayin malama, tana tsara wasu azuzuwan makarantun gaba da sakandare na farko a ƙasar da kuma tsara azuzuwan karatu ga mata masu ƙaramin karfi.

A cikin shekarun 1940, Ransome-Kuti ta kafa ungiyar mata ta Abeokuta kuma ta yi kira ga ’yancin mata, inda ta buƙaci da a samu wakilcin mata a ƙananan hukumomi da kuma kawo ƙarshen harajin rashin adalci ga matan kasuwa. Ta jagoranci zanga-zangar mata har 10,000, wanda ya tilasta wa Alake mai mulki yin murabus na wani ɗan lokaci a 1949. Yayin da tasirin siyasar Ransome-Kuti ya ƙaru, ta shiga cikin harkokin siyasa. Da Masu fafutukar 'yancin kai na Najeriya, halartar taruka da shiga tawagogin ƙasashen ƙetare don tattaunawa kan tsarin mulkin ƙasa. A yayin da ta jagoranci kafa ƙungiyar matan Najeriya, ta yi kira ga a bai wa matan Najeriya ‘yancin kaɗa ƙuri’a, kuma ta zama fitacciyar mamba a ƙungiyar masu fafutukar kare hakkin mata a duniya.

Ransome-Kuti ta sami lambar yabo ta zaman lafiya ta Lenin kuma an ba ta lambar yabo ta zama memba a cikin Order of the Niger saboda aikinta. A shekarunta na baya, ta goyi bayan sukar da ‘ya’yanta ke yi wa gwamnatocin sojan Najeriya. Ta rasu tana da shekaru 77 bayan da ta samu rauni a wani farmaki da sojoji suka kai kan kadarorin iyalinta. 'Ya'yan Ransome-Kuti sun haɗa da: mawaƙi Fela Kuti (Olufela Ransome-Kuti), likita ne kuma ɗan gwagwarmaya. Sai kuma Beko Ransome-Kuti , da ministan lafiya Olikoye Ransome-Kuti .

Cif Fummilayo Ransome-Kuti: (Mahaifiyar Fela Kuti) Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da mace ta farko da ta tuƙa mota a Najeriya.

1, Cif Funmilayo Ransome-Kuti, mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya, malama ce, mai fafutukar siyasa, mai fafutukar kare hakkin mata kuma mai faɗa a ji a Najeriya.

2, Ta kasance mai Tafiye-tafiye mai hazaka. Ta yi balaguro zuwa ƙasashe da yawa a duniya.

3, Kafin Najeriya ta samu 'yancin kai - musamman lokacin yaƙin cacar baka (Cold War) ta yi tafiya zuwa tsohuwar USSR, Hungary da China, inda ta haɗu da Mao Zedong - dan juyin juya halin gurguzu.

4, Ziyarar da ta yi zuwa ƙasashen da ke yankin Gabas ya fusata gwamnatin Najeriya ta ‘yan mulkin mallaka, da kuma gwamnatocin Birtaniya da Amurka.

5, A shekarar 1956, gwamnati ba ta sabunta fasfo ɗin ta ba, saboda an yi imanin cewa manufarta ita ce ta rinjayi ‘yan Nijeriya musamman mata da ra’ayoyi da manufofin gurguzu.

6, An kuma hana ta bizar Amurka saboda gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa ita 'yar gurguzu ce.

7, Ta kasance ɗaya daga cikin wakilan da suka yi shawarwarin samun ‘yancin kan Najeriya daga gwamnatin Birtaniya.

8, Ta kasance wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta Lenin. Gwamnatin Soviet ta na ba da kyautar ga fitattun mutane, fitattun 'yan gurguzu da magoya bayan Tarayyar Soviet waɗanda ba 'yan Soviet ba.

9, A cikin Fabrairu 1978, an jefar da ita daga tagar wani bene mai hawa 3 (Jamhuriyar Kalakuta) mallakar ɗanta mawaƙi, Fela. Hakan ya faru ne lokacin da sojoji dubu suka mamaye ginin. Ta suma kuma daga baya ta mutu a ranar 13 ga Afrilu 1978, daga raunin da ta samu daga faɗowar.

10, Wani lokaci a cikin 2012, don a mutunta ta, ana ɗaukar hotonta domin bugawa a kan takardar kuɗi na N5000. Daga baya gwamnatin Najeriya ta janye shawarar buga Sabon kuɗin N5000.

11, Bayan rasuwarta, ɗan nata Fela ya kai akwatin gawar ta zuwa Barrack Dodan - fadar mulkin Najeriya a wancan lokacin kuma hedkwatar ƙoli na sojan Najeriya ya bar ta a bakin gate. Ya yi hakan ne domin wulaƙanta gwamnatin mulkin soja da Obasanjo ya jagoranta saboda mamaye masa kadarori da ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa. Wannan mamayewa ya zaburar da Fela wajen yin waƙa mai suna “Coffin for Head of State”.

Post a Comment

Previous Post Next Post