Shugaban Majalisar Dattijai Ya Rantsar Da Sabbin Sanatoci Biyu

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Laraba, ya rantsar da sabbin Sanatoci biyu da aka zaba domin cike guraben da suka kasance a baya a mazabun Edo Central da Anambra South a Majalisar Dattawa.

Sanata Joseph Ikpea na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Emmanuel Nwachukwu na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ne suka dauki rantsuwar biyayya da misalin ƙarfe 11:51 na safe a dandalin majalisar.

An gudanar da bukatar rantsuwar ne ta hannun Mukaddashin Magatakardan Majalisar Dattawa, Emmanuel Odo. Ikpea ya fito ne a matsayin wand ha ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Edo Central, yayin da Nwachukwu ya lashe na Anambra South.

Guraben biyu sun zama fanko ne bayan murabus ɗin tsohon Sanatan Edo Central, Monday Okpebholo, wanda ya ajiye mukaminsa domin yin takarar kujerar gwamnan a jiharsa, da kuma rasuwar Sanatan Anambra South, marigayi Ifeanyi Ubah.

A cikin jawabin sa, Akpabio ya bayyana cewa nasu zabe kira ne na hidima ga kasa fiye da sha’anin jam’iyya.

Ya ce, “A yau, an kira ku zuwa aikin kasa. Ba ku kasance sanatocin jam’iyyunku kawai ba, ku sanatocin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ne.”

Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma tabbatar wa sabbin sanatocin cewa za su samu cikakken goyon bayan takwarorinsu yayin da suke sabawa da harkokin dokokin majalisa.

Ya ce, “’Yan uwanku da ke nan za su ci gaba da taimaka muku, domin ku saba da yadda ake gudanar da aikin majalisa. Ina taya ku murna, kuma maraba da ku.”

Daga nan Majalisar ta ci gaba da harkokin zamanta, inda sabbin sanatocin suka zauna a kujerun da aka tanadar musu a dakin ja na majalisar.

Post a Comment

Previous Post Next Post