Afghanistan Da Pakistan Sun Shiga Yarjejeniyar Zaman Lafiya Na Awanni 48 Bayan Rikicin Kan Iyaka

 Ƙasashen biyu sun yarda da dakatar da faɗa bayan ɗaruruwan mutane sun mutu da raunata a rikicin da ya ɓarke a makon da ya gabata.

Afghanistan da Pakistan

Afghanistan da Pakistan sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya na awanni 48, bayan tashin hankali da ya ɓarke a kan iyakar kasashen biyu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne bayan wani rikici tsakanin sojojin ƙasashen biyu a yankin Torkham, inda aka yi musayar wuta na tsawon awanni. Wannan lamari ya tilasta ɗaruruwan mazauna yankin su tsere don neman mafaka.

A cewar jami’an tsaro daga ɓangarorin biyu, yarjejeniyar ta nufin baiwa ɓangarorin damar tattaunawa da kawo cikakken sulhu. Duk da haka, akwai tsoron sabon tashin hankali, ganin cewa irin wannan rikici na kan iyaka ya daɗe yana kawo cikas ga zaman lafiya tsakanin Afghanistan da Pakistan.

Post a Comment

Previous Post Next Post