Ana Kallon Thomas Sankara A Matsayin Wani Gwarzon Matashi Da Ke Kishin Afirika

 A ranar 15 ga Oktoban 1987, sojoji ƙarƙashin jagorancin Blaise Compaoré, wanda ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar jim kaɗan bayan juyin mulki da suka yi wa Thomas Sankara tare da kashe shi. Compaoré ya ci gaba da riƙe madafun iko har zuwa lokacin 2014. A shekarar 2021 an tuhume shi da laifin kisan Sankara da wata kotun soji ta yi.

Thomas Sankara

TARIHIN THOMAS SANKARA

Thomas Isidore Noël Sankara wani hafsan sojan Burkina Faso ne, mai juyin juya hali na Markisanci, kuma mai kishin Afirka wanda ya yi aiki a matsayin shugaban Burkina Faso daga juyin mulkin da ya yi a 1983 zuwa kashe Shi a 1987. A ranar 15 ga Oktoban 1987, wata ƙungiya ɗauke da makamai ta kashe Sankara tare da wasu jami'ai goma sha biyu a wani juyin mulkin da tsohon abokin aikinsa Blaise Compaoré ya shirya.

A ina Aka Haifi Thomas Sankara?

A Yako, wani birni da ke arewacin Burkina Faso, babban birnin lardin Passoré. Yana tazarar kilomita 109 arewa maso yamma da Ouagadougou. Yako dai ya shahara da babban masallacinsa kuma a matsayin mahaifar tsohon shugaban ƙasar Thomas Sankara.  An haifi Thomas Sankara a ne a garin Yako na ƙasar Burkina Faso a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 1949. Mahaifansa 'yan ƙabilar nan ce ta Slimi-Mossi. Thomas ya fara karatunsa na Firamare ne a garin nan na Gaoua, daga bisani kuma ya tafi Bobo-Dioulasso gari na biyu mafi girma a Burkina Faso ɗin domin yin karatunsa na gaba da sakandare.

Mahaifan Thomas Sankara dai sun so ɗan nasu ya zama limamin addinin Kirista, to sai dai hakan ba ta samu ba don bayan kammala karatunsa na gaba da Firamare ya shiga aikin soja inda ya samu horo a matakai da dama. Ya dai shiga horonsa na soja na farko ne a shekara ta 1966. Lokacin da ya ke ɗan shekaru 20 da haihuwa, kuma aka tura shi ƙasar Madagascar domin samun horo, kuma a ƙasar ce ya yi karance-karance ciki kuwa har da litattafan shahararraren marubucin nan Karl max.

Lokacin da ya kammala karɓar horonsa a shekara ta 1972 dai ya ci karo da yaƙin da aka yi tsakanin ƙasarsa da kuma Mali a cikin shekarar 1974. Wannan yaƙi dai na daga cikin abubuwan da suka sanya Sankara ya shahara a wancan lokacin saboda irin jarumtar da ya nuna a lokacin da ya ke fagen daga. Bayan da ƙura ta lafa, a shekara ta 1976 aka naɗa shi kwamandan wata cibiya ta horas da sojin Burkina Faso a garin Po, kuma a ita wannan shekara ce ya haɗu da Blaise Compaore wanda shi ma kamar Sankara tsohon shugaban ƙasar ta Burkina ne.

A cikin shekarar 1981 dai an naɗa Sankara a matsayin sakataren da ke kula da ma'aikatar yaɗa labarai inda a wannan lokacin ya je taron farko na majalisar ministocin ƙasar a kan keke lamarin da jama'a da dama a ƙasar suka yi ta tsokaci a kai. To sai dai bai jima kan wannan matsayi ba don a shekara ta 1982 ya miƙa takardarsa ta murabus bisa dalilin da ya ba da na hana mutane faɗin albarkacin bakunansu.

Bayan da ƙasar ta Burkina Faso ta gamu da juyin mulki a shekarar 1982, an naɗa Sankara firaminista a watan Janairun 1983, sai dai hukumomin Faransa sun sauke shi bayan da wakilin gwamnatin ƙasar da ke kula da harkokin ƙasashen Afirka ya ziyarci ƙasar. Daga bisani kuma ma aka yi masa ɗaurin talala da shi da shugaban mulkin sojin ƙasar na lokacin Manjo Doctor Jean-Baptiste Ouédraogo, lamarin da ya haifar da yamutsi a ƙasar baki ɗaya.

To a cikin shekarar ta 1983 ne dai Thomas Sankara ya zama shugaban ƙasar Burkina Faso lokacin da ya ke da shekaru 33 da haihuwa bayan wani juyin mulki da Blaise Campaore ya shirya. Ƙasar Libya wadda a daidai wannan lokacin ke takun saƙa da ƙasar Faransa dai na daga cikin wanda suka taimaka wa wannan juyin mulki da ya ɗora sankara kan gadon mulkin da ya yi nasara.

Lokacin da ya shugabanci ƙasar dai, ya yi mulki da ya bai wa al'ummar ƙasar 'yancin faɗin albarkacin baki da yaƙi da cin hanci da samar da aiyyukan yi da tabbatar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da ilimi ga 'yan kasa gami da sanya idanu wajen ganin an yaki hamada a kasar ta hanyar samar da dazuka. Kuma lokacin da ya shekara daya a kan gadon mulki ne ya sauya tutar kasar da sauya mata suna daga Upper Volta zuwa Burkina Faso.

Al'ummar Burkina Faso dai a wancan lokacin sun yaba da irin salon shugbancin Thomas Sankara, lamarin da suke kallo a matsayin wata hanya ta maida ƙasar kan gaba a jerin takwarorinta, to sai dai wannan fata nasu ya ci karo da cikas sakamakon hallaka shi da aka yi a wani juyin mulki wanda abokin aikinsa Blaise Campaore ya shirya a ranar 15 ga watan Oktoban shekara ta 1987. Bayan juyin mulki dai mai dakinsa Mariam da yaransa biyu sun arce daga kasar don tsira da ransu

Bayan da ƙura ta lafa dai, Blaise Campaore ya ɗare kan kujerar shugabancin Burkina Faso inda ya jagoranci kasar har zuwa shekara ta 2014 lokacin da ya bar gadon mulki sakamakon jerin zanga-zanga da aka rika yi ta adawa da mulkinsa.

A 'yan shekarun da suka gabata ne dai aka bada sammacin kama Campaore ko ina ya ke a duniya don fuskantar shari'a bisa hannun da aka ce ya ke da shi wajen kashe Thomas Sankara.

A Watan Afrilu na shekarar 2022 wata kotun soja a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasa Blaise Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai sakamakon kama shi da hannu a kisan wanda ya gada Thomas Sankara. An yi wa Compaore shari'a a bayan idonsa yayin da yake gudun hijira. Kana kuma an yanke wa tsohon shugaban sashen tsaro na gwamnatinsa, Hyacinthe Kafando, hukuncin ɗaurin rai-da-rai shi ma.

Ana ganin Sankara a matsayin wani gwarzo a fadin Afirka saboda aƙidarsa ta ƙyamar Turawan Mulkin Mallaka.

Post a Comment

Previous Post Next Post