Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta ƙaryata rahotanni da ke cewa ta kafa wani kwamiti domin karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, APC ta bayyana rahoton da shafin confidentialreporters.blogspot.com ya wallafa a matsayin “ƙarya ce kuma mai cike da yaudara.”
“APC ta Zamfara ba ta taɓa tuntuɓar PDP ko Gwamna Dauda Lawal ba domin ya shiga jam’iyyarmu,” in ji Gusau.
Jam’iyyar ta ce ba ta gamsu da yadda Gwamna Lawal ke gudanar da mulki ba, tana mai nuni da nasarar da ta samu a zaben cike gurbi na Kaura Namoda South da aka gudanar a ranar 16 ga Agusta a matsayin shaida cewa karɓuwar PDP a jihar tana raguwa.
APC ta kuma bayyana cewa ɗan takarar PDP a wannan zaɓe, tare da wasu daga cikin magoya bayansa, tuni suka koma jam’iyyar APC.
“Ba mu buƙatar ƙaryar wata kafar labarai mara inganci don tabbatar da goyon bayanmu daga ƙasa,” in ji jam’iyyar.
A ƙarshe, APC ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin ƙarya ɗin, tare da neman a riƙa dogaro da hanyoyin sadarwar jam’iyyar na hukuma domin samun sahihan bayanai.