A wata sanarwa da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa (NCoS) ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa matakin ya zama wajibi ne domin kare tsaron gidajen gyaran hali da kuma hana faruwar ɓaraka yayin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 20 ga Oktoba, 2025.
Mai magana da yawun hukumar, Umar Abubakar, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya jaddada cewa gidajen gyaran hali wurare ne masu taƙaitaccen shiga da fice, inda ya gargaɗi jama’a da su kauce musu idan ba su aiki a can.
“Dangane da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da aka shirya, jama’a suna sanarwa cewa dukkan gidajen gyaran hali an ayyana su a matsayin yankunan haɗari,” in ji sanarwar.
“Duk wanda ba shi da izinin aiki a irin waɗannan wurare ya guje musu domin kauce wa abin da ka iya faruwa.”
Hukumar ta buƙaci ‘yan ƙasa da su haɗa kai da jami’an tsaro, su nuna biyayya da nutsuwa, tare da mutunta matsayin da aka bai wa gidajen gyaran hali domin tabbatar da zaman lafiya da tsari a ƙasa.
An shirya zanga-zangar ne ƙarƙashin jagorancin mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, Omoyele Sowore, domin matsa wa gwamnati lamba ta saki Nnamdi Kanu, wanda ke tsare tun daga shekarar 2021 bisa tuhumar ta’addanci da cin amanar ƙasa.
An kama Kanu ne a shekarar 2021 bayan guduwarsa daga Najeriya, kuma har yanzu yana cikin tsaka mai wuya — wasu na kallonsa a matsayin jarumin ‘yanci, yayin da gwamnati ke daukarsa barazana ga tsaron ƙasa.
Tsarewar Kanu na cigaba da haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a, musamman bayan hukuncin Kotun Daukaka ƙara a 2022 da ta umarci a sake shi, wanda daga baya Kotun Koli ta dakatar da aiwatarwa.