Google Ta Ba Daliban Jami’a A Afrika Damar Amfani Da Google AI Pro Kyauta Na Tsawon Shekara Daya

Kamfanin fasaha na Google ya sanar da sabon shirin tallafi ga daliban jami’a a kasashen Afrika, wanda zai basu damar amfani da Google AI Pro kyauta na tsawon shekara daya, domin ƙarfafa ilimi da ƙwarewa a fannin fasahar wucin-gadi (AI).

Shirin, wanda ake kira Google AI Pro Plan for Students, zai kasance ne ga ɗaliban da shekarunsu suka haura 18, daga kasashen Najeriya, Kenya, Ghana, Rwanda, Afrika ta Kudu da Zimbabwe.

A cewar Google, manufar shirin ita ce gina ƙwarewar matasan Afrika a ɓangaren AI, tare da baiwa dalibai damar amfani da sabbin kayan aikin kamfanin don karatu, bincike, da ƙirkire-ƙirkire.

Google Na Son Taimaka Wa Matasa Su Zama Masu Ƙirkira

Da yake magana kan wannan ci gaba, Manajan Darakta na Google a yankin Afrika, Alex Okosi, ya ce matasa a nahiyar na taka muhimmiyar rawa wajen kawo sabbin abubuwa a fannin fasaha.

“Muna ganin sabon salo na ƙirƙire-ƙirƙire daga matasan Afrika. Ta hanyar ba su damar amfani da kayan aikin AI na zamani, muna son su yi fice a karatunsu kuma su zama masu gina makomar duniya. Wannan shiri yana nufin bai wa kowa damar amfani da fasaha tare da samar da ƙwarewar da za ta sa daliban Afrika su iya gogayya a matakin duniya,” in ji shi.

Abubuwan Da ke Cikin Shirin Google AI Pro

Google AI Pro Plan yana tattare da wasu mahimman kayan aiki da suka dace da buƙatun daliban jami’a, ciki har da:

  • Koyo da bincike mai zurfi: Tana amfani da fasahar Guided Learning wacce ke taimaka wa ɗalibai wajen taƙaita takardun bincike, gyara lambar kwamfuta (code), da kuma fahimtar matsaloli masu rikitarwa cikin sauƙi.

  • Deep Research: Tana tattara bayanai daga daruruwan shafukan intanet cikin ƴan mintuna, domin samar da rahotanni masu tushe don karatu da rubuce-rubuce.

  • Tsari da kirkira: Ana amfani da NotebookLM wajen tsara bayanai da haɗa ra’ayoyi, sannan Veo 3 tana juyar da rubutu ko hoto zuwa gajeren bidiyo mai inganci domin gabatarwa.

  • Ajiyar bayanai: Dalibai za su samu 2TB na ajiya a Google Drive, Gmail, da Photos domin adana takardu, bayanan bincike, da ayyukan kirkira. 

    Lokacin Rajista Da Yadda Ake Samun Damar Amfani Da Shi

    Alex Okosi ya bayyana cewa, daliban jami’a daga Ƙasashen da abin ya shafa za su iya tabbatar da matsayin su na dalibi domin samun damar yin rajista cikin sauƙi.
    Ya ƙara da cewa tsarin yana buƙatar dalibi ya tabbatar da biyan kuɗi (ba tare da an cire masa kudi ba). Shirin zai kasance a buɗe tsawon kwanaki 60 — daga 7 ga Oktoba, 2025, zuwa 9 ga Disamba, 2025

    Ci Gaban Da ke Ƙara Tabbatar Da Jajircewar Google Ga Afrika

    A cewar Okosi, wannan shiri yana ci gaba da nuna yadda Google ke goyon bayan bunƙasar dijital a nahiyar Afrika, ta hanyar shirye-shirye kamar Google for Startups Accelerator Africa da Digital Skills for Africa, waɗanda suka taimaka wajen horas da miliyoyin matasa da ‘yan kasuwa a nahiyar.

  • Post a Comment

    Previous Post Next Post