Macron Ya Gabatar Da Sabuwar Gwamnati Kafin Wa’adin Kasafin Kudi

Macron

Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya sanar da sabuwar gwamnati yayin da ƙasar ke shirye-shiryen gabatar da sabon kasafin kuɗi kafin cikar wa’adin majalisa. Sabon tsarin ministocin ya haɗa da tsofaffin jami’ai da sabbin fuska domin kawo daidaito a cikin gwamnatin da ke fuskantar matsin lamba daga ‘yan adawa.

Rahotanni sun nuna cewa sabon kasafin kuɗin zai mai da hankali ne kan farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar da kuma tallafawa jama’a da farashin kayan masarufin da ya daɗe yana ƙaruwa.

Masu sharhi sun bayyana cewa wannan sabon tsarin gwamnati wani yunƙuri ne na Macron domin ƙarfafa matsayinsa kafin zaben majalisa mai zuwa da kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa ta ci gaba da samun goyon bayan jama’a.

Post a Comment

Previous Post Next Post