Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jimaminsa matuƙa kan rasuwar Jakadiya Joy Uche Angela Ogwu, wadda ta rasu tana da shekaru 79.
Jakadiya Ogwu, tsohuwar Ministar Harkokin Waje kuma Jakadiya mai wakiltar Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York daga watan Mayu 2008 zuwa Mayu 2017, ta kasance gogaggiyar jakadiya mai zurfin fahimta.
Ta yi aiki a matsayin Darakta-Janar ta Cibiyar Harkokin Ƙasashen Waje ta Najeriya (NIIA), inda ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa manufofin ƙasashen waje na Najeriya da karatun dangantakar ƙasa da ƙasa.
Jakadiya Ogwu ta jagoranci Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya sau biyu — a watan Yuli 2010 da kuma Oktoba 2011 — inda ta nuna ƙwarewa, jajircewa da kishin ƙasa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba wa marigayiyar bisa wakiltar Najeriya da ƙwazo da gaskiya, tare da jajircewa wajen neman zaman lafiya a duniya, rage makamai, tsaron ƙasa da ƙasa da kuma haɓaka haƙƙin mata.
Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga ’ya’ya biyar da jikokinta, ’yan uwanta mata da maza, duka dangin Ogwu, da al’ummar diflomasiyya da ilimi baki ɗaya, bisa rashi mai girma da suka yi.
“Ina cewa Najeriya ta rasa bajintacciyar mace wadda ta kai matsayi mafi girma a aikinta ta hanyar ƙwazo da jajircewa,” in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban ƙasa ya yi addu’ar Allah Ya ji ƙan marigayiya, Ya kuma ba iyalanta da duk masu jimami haƙuri.