Sojin Sama Sun Tarwatsa Masu Hakar Man Fetur Ba Bisa Ka’ida Ba a Rivers

Port Harcourt – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai farmaki cikin tsari bayan samun bayanan sirri a ranar 7 ga Oktoba, 2025, inda ta tarwatsa wasu sansanonin tace man fetur na haramtacciyar hanya da ke cikin kogunan ƙaramar hukumar Etche, a Jihar Rivers.

NAFMai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa hare-haren saman sun kasance ɓangare ne na ci gaba da ayyukan yaƙi da satar man fetur da NAF ke Port Harcourt – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai farmaki cikin tsari bayan samun bayanan asiri a ranar 7 ga Oktoba, 2025, inda ta tarwatsa wasu sansanonin tace man fetur na haramtacciyar hanya da ke cikin kogunan ƙaramar hukumar Etche, a Jihar Rivers.

Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa hare-haren saman sun kasance ɓangare ne na ci gaba da ayyukan yaki da satar man fetur da NAF ke gudanarwa a yankin Niger Delta.

Ejodame ya ce jiragen saman NAF sun gano wajen tace man haramtacciyar hanya da aka ɓoye a cikin dausayi mai cike da itatuwa kusa da garin Owaza. Ya kara da cewa wurin ya kasance nesa da mazauna mutane, kuma an tabbatar da sahihancinsa ta hanyar bayanan leƙen asiri da binciken sama.

“Sojojinmu sun kai harin cikin daidaito, inda suka lalata wuraren gaba ɗaya tare da dakatar da ayyukan haramtattun masu tace man,” in ji Ejodame. 

Sai dai, bayan kammala harin, Ejodame ya ce an samu rahoton wani rukuni da ya yi ikirarin cewa harin saman ya shafi wani wajen yin giya ta gargajiya a ƙauyen Umuebele, duk da cewa ba a samu rahoton asarar rai ba.

“A bisa tsarin ta na Civilian Harm Mitigation and Response Action Plan (CHMR-AP), rundunar ta fara bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin,” in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa NAF za ta ci gaba da bin ka’idojin aikin soja na ƙasa da ƙasa, tare da tabbatar da gaskiya, adalci da ɗaukar alhakin dukkan ayyukanta.

A cewarsa, rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, da kuma ƙarfafa yaƙi da satar mai da gurɓata muhalli a yankin Niger Delta. da tabbatar da gaskiya, adalci da ɗaukar alhakin dukkan ayyukanta.

A cewarsa, rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, da kuma ƙarfafa yaƙi da satar mai da gurɓata muhalli a yankin Niger Delta.

Post a Comment

Previous Post Next Post