Yadda Za A Gane Cutar Basir Da Kuma Matakin Da Ta Kai

 Basir ko Ɗankanoma, sunan Hausa ne na cutar da ake kira da Piles ko Hemorrhoids a Turanci. Ɗankanoma (Basir) shi ne kumburin jijiyoyin jini a cikin ƙananan hanji (rectum) ko kuma a bakin ciki. Wannan kumburi da ke kama jijiyoyin jini na iya kasancewa mai raɗaɗi, ciwo, ko kuma fitar da jini lokacin yin bayan gida, haka kuma ana iya samun tashin zuciya na tsawon lokaci. Sannan za a iya jin wasu alamomi kamar haka: fitowar jini lokacin yin bayan gida, kumburi ko wani abu mai kamar ƙulli a bakin ciki, ciwo ko zafi a wurin yin bayan gida, ƙaiƙayi (itching) a bakin dubura da sauransu.

Wasu lokutan mutum yana fama da basir, amma bai san a wanne mataki cutar ta kai ba — ko mai sauƙi ce, ko mai buƙatar tiyata ce. Ga yadda zaka gane matakin basir ɗinka a sauƙaƙe a gida, kafin ka je asibiti:


Mai Cutar Basir

1. Mataki Na 1 — (Basir Mai Sauƙi)

Alamomi:

• Jin kaikayi  a wajen dubura

 •  fitar jini  kadan kadan lokacin bayan gida

 • Wani dan ƙurji a wajen dubura

A wannan matakin, basir ɗin yana ciki sosai bai  fito ba. Wannan magani da canza wasu abubuwa na yau da kullum kan iya magance shi

2. Mataki Na 2 — (Basir Mai Fitowa da Kansa Sannan Ya Koma da Kansa)

Alamomi:

 • Lokacin bayan gida, za ka ga basir ya fito amma yana komawa da kansa

 • Zafin dubura ko jin nauyi a wajen. A wannan matakin magani zai iya warkar da shi

3. Mataki Na 3 — (Basir da In Ya Fito Ba Ya Komawa da Kansa, Wato Yana  Bukatar A Maida Shi  da Hannu)

Alamomi:

 • Basir yana fitowa sosai idan an je bayan gida, kuma ba ya komawa sai idan an mayar da shi da hannu 

 • Jin zafi sosai, kumburi ko kaikayi mai tsanani

A mafi yawan lokuta idan akai sa'a, magani da shiga ruwan gishiri na iya warkar da shi, amma kuma wani lokacin magani kadai ba ya wadatarwa sai an yi aiki.

Mataki Na 4 Hudu (Basir Mai Tsanani)

Alamomi:

 • Basir ya fito waje gaba ɗaya kuma ya ƙi komawa ko da an mayar da shi da hannu.

 • Jin zafi mai tsanani, kumburi, jini mai yawa ko ciwo lokacin daka zauna. Mafi lokuta anfi bada shawara ayi aiki inyakai wannan matakin

Post a Comment

Previous Post Next Post