"Wani Ma Zai Ce Ai Yanzu Babu Nijeriya" In ji Sanata Dino Malaye.
Tsohon Sanatan ya bayyana haka ne a firarsa da ya yi da Umaima Abdulmumini ta BBC Hausa.
A firar ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bai cika ko alƙawari ɗaya da ya ɗauka ba, ya ƙara da cewa shugaban ya yi alkawarin rage kashe kuɗaɗe amma sai ga shi ya buge da sayen jirgin sama har ma da na ruwa.
A firar tasa ya bayyana cewa ya fita ya yo karatun Law na tsawon shekara 4, sannan ya je Law School ya yi shekara ɗaya domin zama cikakken lauya, a ɓoye don kar a yi masa Nijeriya, bayan da ya bayyana cewa Nijeriyar cike take da mahassada da 'yan baƙin ciki.