Za A Iya Gudanar Da Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Watan Nuwamba 2026

Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ƙaddamar da shirin sauya jadawalin zaɓe domin a gudanar da babban zaɓen Najeriya  na shugaban ƙasa da na gwamnoni  a watan Nuwamba 2026, wato watanni shida kafin ƙarshen wa’adin gwamnati mai ci yanzu.

Wannan na cikin daftarin gyaran dokar zaɓe (Electoral Act Amendment Bill 2025) da aka gabatar a zaman sauraron jama’a da kwamitocin zaɓe na majalisar dattawa da ta wakilai suka shirya a Abuja ranar Litinin.

A cewar daftarin, “Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da gwamna ba fiye da kwanaki 185 kafin ƙarshen wa’adin wanda ke rike da muƙamin ba.”

Wannan na nufin zaɓen zai fado ne a watan Nuwamba 2026 — kafin ranar 29 ga Mayu 2027, lokacin da ake sa ran rantsar da sabbin shugabanni.

Shugaban Kwamitin Zaɓe na Majalisar Wakilai, Hon. Adebayo Balogun, ya bayyana cewa manufar gyaran ita ce “a tabbatar an kammala dukkan shari’o’in zaɓe kafin a rantsar da sabbin shugabanni.”

Majalisar tana kuma shirin gyara Sashe na 285 da 139 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, domin rage lokacin shari’ar zaɓe daga kwanaki 180 zuwa 90 a matakin kotun sauraren ƙorafe-ƙorafen zaɓe, da daga 90 zuwa 60 a matakin kotun ɗaukaka ƙara — ta yadda duka shari’ar ba za ta wuce kwanaki 185 ba.

Haka kuma, an gabatar da ƙudurin ba da damar yin zaɓe da wuri ga wasu rukuni na ’yan Najeriya, ciki har da jami’an tsaro,ma’aikatan INEC, manema labarai da masu sa ido, aƙalla kwanaki 14 kafin ranar zaɓe.

Muhimmin ɓangare na gyaran shi ne tilasta watsar da sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki, inda sabuwar ƙa’ida ta 60(5) ta tanadi cewa:
“Jami’in zaɓe zai aika da sakamakon, ciki har da adadin masu kada kuri’a, zuwa matakin tattarawa na gaba ta lantarki da kuma ta hannu.”

Doka ta kuma tanadi hukuncin daurin shekara ɗaya ko tara ₦1 miliyan ga jami’in da ya bai wa mutane takardar kuri’a ko takardar sakamako ba tare da sa hannu ko hatimi ba.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), wacce Farfesa Abdullahi Zuru ya wakilta, ta nuna goyon bayanta ga kudirin  musamman ɓangaren zaɓen lantarki da watsar da sakamako ta e-transmission  tana mai cewa wannan zai ƙara sahihanci da rage rigingimun bayan zaɓe.

A watan Yuli, aka samu ra’ayoyi masu karo da juna kan shirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman a gudanar da dukkan zaɓe a rana guda a 2027. 

Jam’iyyun adawa irin su PDP, Labour Party, ADC, da NNPP sun nuna goyon baya, yayin da APC mai mulki ta yi adawa, tana gargaɗin cewa hakan na iya haifar da matsaloli.

Wannan shirin na ƙarƙashin Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Wakilai da mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu, ke jagoranta  kuma yana daga cikin sakamakon tattaunawa da aka gudanar a faɗin sassan ƙasar shida.

Idan aka amince, za a tilasta wa INEC gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, majalisar da zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, majalisar tarayya da majalisun jihohi a rana guda — wani mataki da ake ganin zai rage kuɗin gudanar da zaɓe da kuma tasirin tasowa daga sakamakon wani zaɓe zuwa wani.

Post a Comment

Previous Post Next Post