Ahmad Babba Kaita Ya Yi Kira Ga Shuwagabannin Nijeriya Da Su Dauki Mataki Kan Amurka Saboda Babu Wata Hujja A Kan Zargin Da Take Wa Nijeriya

" Assalamu alaikum,

Kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yai na cewar zai ɗauki matakin soji a kan Najeriya saboda zargin da gwamnatinsa ta yi na cewar wai ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla abin takaici ne matuƙa. Da fari dai ba wata hujja da Amurka ke da ita kan wannan zargi da take yi, domin babu wani wajen da aka yi wa Kirista kisan gilla kamar yadda suke da'awa.

Tsohon Sanata A Nijeriya, Ahmad Babba Kaita

Bai kamata a ce mun zuba idanu a wayi gari wata ƙasa kawai ta ce za ta yaƙe mu kan lamarin da ko kusa babu shi ba. Ni a ganina wannan mataki na Amurka keta alfarmar 'yancin da ƙasarmu take da shi ne kuma ba abu ne da ya kamata mu lamunta ba.

A don haka ina kira ga mahukuntan Abuja da su tashi tsaye wajen turjewa wannan cin mutuncin da Amurka ke ƙoƙarin yi, sannan su ci gaba da zage damtse wajen ɗaukar matakai na magance ƙalubalen tsaron da ƙasarmu ke fuskanta wanda ya shafi kowa, ba wai Kiristoci kadai ba."

Post a Comment

Previous Post Next Post