Sanata Rabi'u Musa Kwanakwaso Bayyana Damuwarsa Kan Kalaman Shugaban Ƙasar Amurka Kan Najeriya

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi dangane da zargin kisan kiyashi da ake cewa ana yi wa Kiristoci a Najeriya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Kwankwaso ya ce ya lura da yadda Shugaban Ƙasar Amurka ke ta ƙara yin tsokaci kan lamurran cikin gida na Najeriya, musamman bayan sanya sunan ƙasar cikin jerin ƙasashen da ake kira “ƙasashe masu matuƙar damuwa” (country of particular concern).

Kwankwaso ya jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yancin kai, wacce ke fuskantar matsalolin tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasa, ba tare da bambancin addini, ƙabila, ko ra’ayin siyasa ba.

A cewarsa, maimakon Amurka ta rika fitar da kalaman barazana, ya dace ta taimaka wa Najeriya da kayan aikin zamani da fasaha don yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

“A maimakon yin barazana da ka iya kara raba kan al’umma, ya fi dacewa Amurka ta taimaka wa hukumomin tsaronmu da ingantattun kayan aiki da fasahar zamani domin shawo kan waɗannan ƙalubale,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na dindindin da kuma wakilai na musamman da za su kare muradun ƙasar a matakin ƙasashen duniya.

“Ya kamata gwamnatin Najeriya ta naɗa wasu ƙwararrun jakadu daga cikin fitattun diflomatanta domin tattaunawa da gwamnatin Amurka, tare da tabbatar da cewa an naɗa jakadu na dindindin da za su wakilci muradun ƙasarmu a duniya,” Kwankwaso ya ƙara da cewa.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance tsintsiya ɗaya, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai a kan rarrabuwar kawuna.

“’Yan uwana ‘yan ƙasa, wannan lokaci ne da ya kamata mu ɗora kan haɗin kai da ƙaunar juna fiye da rarrabuwa. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post