A ƙoƙarin inganta lafiya a jihar Zamfara, Gwamnatun jihar ta samar da wayoyin hannu domin inganta aikin tallafin lafiya ga ma'aikatan jihar. Kamar yadda ma'aikatan gwamnatin tarayya ke amfana da tallafin lafiya wanda sukan biya kuɗi kaɗan idan lalurar rashin lafiya ta kai shi ko iyakansa asibiti.
Babban sakatare a ma'aikatar lafiya malam Bashiru Sirajo Gusau ya ce:
" Raba wayoyin yana cikin ƙoƙarin ƙoƙarin gwamna Dauda Lawal na inganta fannin lafiya , da kuma kawo sassafci ga rayuwar ma'aikata da kuma iyalansu. Ya ƙara da cewa raba wayoyin zai sa hukumar ta riƙa samun sahihan bayanai game da yawan ma'aikatan da ke zuwa kowace asibiti a kowace rana".
Sakataren gudanarwa na hukumar ZANCHEMA ( Zamfara State Healthcare Contributory Management Agency ) malam Ahmad Sale ya ce:
" Maimakon a ce, sai an buɗa wani littafi wajen neman sunan mutum sai kawai a tafa sunan ga waya sai ya fito. Kuma ofis za su samu bayanan".
Baya ga wannan cigaba, gwamnatin jihar Zamfara ta ɗaga darajar wasu asibitoci a wasu yankunan jihar domin sauƙaƙa wa al'ummar yankunan game da abin da ya shafi neman lafiya.