Hare-haren ƴanbindiga kan makarantu da sace ɗalibai a yankin arewacin Najeriya sun zama jiki, abin da ka iya jawo koma-baya a fannin ilimin yankin, wanda da ma yake fama da yaran da ba su zuwa makaranta.
A lokuta da dama ƴanbindigar kan kai hare-hare kan makarantu tare da sace ɗalibai, kamar yadda muka gani a jihohin Borno da Yobe da Zamfara da Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi.
Na baya-bayan nan su ne satar ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi daga sakandaren Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga, da kuma ɗaliban firamare da nazire da aka sace a St. Mary da ke jihar Neja.
Matsalar ta sa jihohin Arewa sun rufe makarantu masu yawa na firamare da sakandire a jihohin da matsalar ta fi ƙamari.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ta gano cewa akwai makarantun firamare da na sakandire aƙalla 180 da aka rufe sakamakon matsalolin tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.
Shi ma kamfanin Beacon Security mai bincike kan tsaro a yankin Sahel ya gano cewa daga 2020 zuwa 2025 an rufe makarantu kimanin 210 sakamakon matsalar tsaro a arewacin Najeriya.
A wata hira da BBC, shugaban kamfanin, Kabiru Adamu, ya ce a wasu wuraren an sauya wa ɗaliban da lamarin ya shafa makarantu, yayin da a wasu wuraren kuma ɗaliban suka haƙura da karatun.
A wasu jihohin an mayar da wasu makarantun sansanin ƴangudun hijira, yayin da wasu suka koma sansanin jami'an tsaro, wasu kuma suka koma sansanin ƴanbindigar.
Rufe makarantu ya jefa miliyoyin yara cikin halin rashin zuwa makaranta domin samun ilimi, lamarin da ya sa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin ya ƙaru matuƙa.
Alƙaluman da asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar a 2024 sun nuna cewa yara miliyan 18.3 ne ba su zuwa makaranta a Najeriya, kashi 66 cikin 100 na yaran a arewa maso yamma da arewa maso gabas suke.
Ko mece ce makomar waɗannan yara da ma al'ummar yankin baki ɗaya?
A wasu jihohin an mayar da wasu makarantun sansanin ƴangudun hijira, yayin da wasu suka koma sansanin jami'an tsaro, wasu kuma suka koma sansanin ƴanbindigar.
Rufe makarantu ya jefa miliyoyin yara cikin halin rashin zuwa makaranta domin samun ilimi, lamarin da ya sa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin ya ƙaru matuƙa.
Alƙaluman da asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar a 2024 sun nuna cewa yara miliyan 18.3 ne ba su zuwa makaranta a Najeriya, kashi 66 cikin 100 na yaran a arewa maso yamma da arewa maso gabas suke.
Ko mece ce makomar waɗannan yara da ma al'ummar yankin baki ɗaya?
Dr Aliyu Usman Tilde tsohon kwamishinan ilimi ne a jihar Bauchi kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya. Ya ce babbar barazana ce a yanzu a ce yaro ba ya zuwa makaranta a wannan zamani da ake ciki.
''Matsawar mutum bai yi ilimi ba, to bambancinsa da dabba babu yawa'', in ji shi.
Ya ce duk wanda ya tashi babu ilimin addini ko na zamani to rayuwarsa na cikin gagari.
''Hasali ma zai zame wa al'ummar da yake rayuwa a cikinsu gagarumar matsala'', kamar yadda ya bayyana.
Shi ma Dakta Kabiru Adamu ya ce hakan zai shafi ingancin rayuwar yaran, saboda rashin ilimin, wanda shi ne gishirin rayuwa.
A cewar Dr Tilde, akasarin wuraren da ake samun irin wannan matsalar sana'o'in wurin ba su wuce noma da kiwo.
''Kuma ko shi noma da kiwon idan babu ilimi ba za su yiwu yadda ake buƙata ba'', in ji shi. Ya ci gaba da cewa duk sana'ar da mutum zai yi a yanzu tana buƙatar aƙalla ilimin boko na matakin farko.
"Galibi irin waɗannan yara za su ƙare cikin halin rashin sanin ciwon kai da shaye-shaye da sace-sace da ma dabar siyasa kamar. Babu wata gwagwarmayar rayuwa da za su iya yi domin su taimaki kansu ko al'umma, saboda ba su da tushe mai kyau.
"Babu wani fata da yaran suke da shi zuwa gaba matuƙar ba su samu ilimi ba, saboda babu wani muradi da za su sanya a gaba."
Hausawa na cewa yara manyan gobe, kuma idan yaran ba su samu ilimi ba akwai yiwuwar gobe za a samu manyan jahilai, kamar yadda masana ke bayani.
Dr Tilde ya ce rashin ilimin yara babu abin da zai haifar sai cutarwa ga al'ummar gobe.
''Rayuwa ce za a samu ta cibaya, saboda babu masu ilimi a cikin al'ummar'', a cewarsa.
Sannan ya ce aikata miyagun laifuka za su yawaita a yankin, matsawar ba a magance wannan matsala ba.
''A yankunan da ake da wadatuwar ilimi ma ya aka ƙare da shaye-shaye da sace-sace, da bangar siyasa, ballantana al'ummar da ba su yi karatu ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
A nasa ɓangare, Dr Kabiru Adamu ya ce abin da hakan ke nufi shi ne nan gaba yankin zai fuskanci koma-baya tsakanin takwarorinsa da sauran yankunan ƙasar.
Me ya kamata gwamnati da al'umma su yi?
Dr Tilde ya ce babban abin da ya kamata al'umma su yi shi ne zaman lafiya.
''Abu na farko shi ne, al'umma su yarda su zauna lafiya da juna. Babu abin da ya fi zaman lafiya, idan babu zaman lafiya babu abin da za a iya yi ciki har da zuwa makaranta'', in ji shi.
Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum din ya ce yankin arewacin Najeriya yanki ne daya yi fice da tarihin zaman lafiya a baya.
''Amma a yanzu ga shi al'amura na neman sauyawa, ana neman a dagula yankin ta hanyar kawo tashin hankali, don haka zaman lafiya shi ne babban abin da ya kamata a samar tukunna'', in ji shi.
A gefe guda, yana da kyau gwamnati ta yi bakin ƙoƙarinta wajen smar da tsaron yankin domin yara su je makaranta.
Haka ma, Dr Kabiru Adamu ya ce yana da kyau masu ruwa da tsaki da ƴankasuwa su yi iya baƙin ƙoƙarinsu don ganin sun kawo gyara a yankiin.
''Matsalar ba ta gwamnati ba ce ita kaɗai. Kowa da irin rawar da ya kamata ya taka domin magance wannan matsalar'', in ji shi.