Gwamnatin Chadi Ta Kulle Iyakar Kasarta Da Nijeriya

Gwamnatin kasar Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Najeriya nan take, tana mai bayyana damuwar tsaro sakamakon rahotannin da ke nuna yiwuwar shirin mamayar sojojin Amurka a yankin Yammacin Afirka.

Sojojin Chadi

Zagazola Makama ya rawaito cewa majiyoyin tsaro daga birnin N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya bayar da umarnin kulle iyakar kasar gaba ɗaya da Najeriya bayan bayanan leƙen asiri sun nuna cewa wasu mayakan ta’addanci daga arewacin Najeriya na shirin tserewa zuwa cikin yankin Chadi.

Majiyoyin sun ce an sanya dakarun sojojin Chadi cikin shirin ko-ta-kwana, inda aka baza sojoji da motocin yaƙi masu sulke a muhimman hanyoyin da ke haɗa kasashen biyu.

An ruwaito shugaban kasar yana gargadi da cewa, “ba wata ƙungiyar makamai ko ƙasar waje da za a bari ta shiga ƙasar Chadi cikin kowace irin dabara.”

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin tashin hankali a yankin, tare da ƙaruwa jita-jitar cewa Amurka na gudanar da wasu ayyukan soja a wasu sassan Yammacin Afirka.

Masu nazarin tsaro sun bayyana cewa rufe iyakar na da nufin kare cikakken ikon Chadi da kuma hana yiwuwar shiga ƙungiyoyin makamai da za su iya amfani da rashin kwanciyar hankali a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post