Sojojin Nijeriya ƙarƙashin Rundunar Sintirin Hadin Gwiwa, MESA, ƙarƙashin Bataliya ta 3, sun fatattaki harin da ƴan ta’adda suka kai kan al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka kashe mutane 19 daga cikin maharan.
Daily Trust ta rawaito cewa sojojin, tare da haɗin gwiwar wasu jami'o'in tsaro, sun yi artabu da ƴan bindigar bayan samun bayanan sirri game da motsinsu a yankunan Ungwan Tudu, Ungwan Tsamiya, da Goron Dutse, misalin ƙarfe 5:00 na yamma, ranar 1 ga Nuwamba, 2025.
A cewar wata sanarwa da Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji na Bataliya ta 3, ya fitar, sojojin sun gaggauta fita don dakile harin, inda suka yi wa ‘yan bindigar kwanton bauna yayin da suke wucewa akan babura, inda aka to ka bata-kashi.
“A yayin fafatawar, an kashe ‘yan bindiga 19 yayin da aka kwato babura da dama da kuma wayoyi guda biyu daga hannun su,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasa rayukansu a yayin yakin.
Kyaftin Zubairu ya ce, ana ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri a yankin domin kare al’ummomin da ke cikin zaman ɗar-ɗar, waɗanda aka dade ana kai wa hare-hare da satar shanu da sauran laifuffuka.
