Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa ƙasarsa na iya kai wa Najeriya hari ta sama ko ta ƙasa idan har gwamnati ta kasa ɗaukar mataki kan abin da ya kira kisan Kiristoci da ake yi a ƙasar.
Trump ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a fadar White House, inda ya ce Amurka ba za ta yi shiru ba idan har Kiristoci a Najeriya suna ci gaba da fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda.
Shugaban ya ce an sha kai masa rahotanni da dama game da tashe-tashen hankula da kisan jama’a a yankunan Arewa, inda ya zargi gwamnati da rashin tsananta doka da kare ‘yan ƙasa. “Idan har Najeriya ta kasa kare mutanenta, musamman Kiristoci da ake kashewa saboda addini, to za mu ɗauki matakin da ya dace. Wannan matakin zai iya zama hari ta sama ko ta ƙasa,” in ji Trump.
Wannan barazana ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin manyan ƙasashen duniya, yayin da gwamnatin Najeriya ta ce tana gudanar da bincike da kuma aiki kafada da kafada da Amurka don kawo karshen ta’addanci a ƙasar.
Sai dai wasu masana harkokin tsaro sun ce barazanar Trump na iya ƙara dagula alaƙa tsakanin Najeriya da Amurka, musamman idan aka ɗauke ta a matsayin tsoma baki cikin harkokin cikin gida.