Kungiyoyin Musulmi Sun Yi Zanga-Zangar Kin Kalamun Trump A Kano

Ɗaruruwan ƙungiyoyin Musulmi da magoya bayansu sun gudanar da zanga-zanga a Kano ranar Asabar, suna nuna adawa da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya zargi Najeriya da yin shiru kan “kisan Kiristoci” tare da barazanar kai farmakin soja.

Masu zanga-zangar, da suka fito daga Masallacin Juma’a na Kano suka nufi Sabon Gari, suna riƙe da allunan rubutu masu ɗauke da hoton Trump tare da rera waƙoƙi na adawa da Amurka cikin harshen Hausa. Sun bayyana kalamansa a matsayin “ƙarya mai hatsari” da ke iya tayar da fitinar addini a ƙasa.

Trump a makon da ya gabata ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake kira Countries of Particular Concern saboda zargin take hakkin Kiristoci, tare da umartar Ma’aikatar Tsaron Amurka da ta shirya zaɓin kai farmaki idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki.

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani cikin gaggawa, inda Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana kalaman Trump a matsayin “marasa tushe,” yana mai cewa matsalar tsaro ta shafi Musulmi da Kiristoci baki ɗaya. Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce bayanin Amurka bai dace da hakikanin yanayin tsaron kasar ba.

Kungiyoyin Musulmi a Arewacin Najeriya sun zargi Trump da ƙoƙarin amfani da addini a matsayin makami wajen raba kan ’yan Najeriya.

A nasa ɓangaren, Fasto Enoch Adeboye, Jagoran Cocin Redeemed, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi sulhu da Amurka ta hanyar diflomasiyya tare da neman wa’adin kwanaki 90 domin nuna ci gaban da ake samu wajen yaƙi da ta’addanci. Ya gargaɗi cewa rashin haƙuri na iya jefa ’yan kasa cikin wahala.

Ƙasashen Sin da Rasha, tare da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), sun nuna adawa da duk wani yunƙurin kai farmaki a Najeriya, suna mai jaddada muhimmancin mutunta ’yancin kasar da yin tattaunawa maimakon barazana.

Najeriya dai na fama da matsalar tsaro ta tsawon shekaru, daga ta’addancin Boko Haram a arewa maso gabas, zuwa rikice-rikicen kabilanci a tsakiyar kasar, da kuma hare-haren ’yan bindiga a arewa maso yamma. Rahoton Amnesty International ya nuna cewa sama da mutum 1,800 aka kashe a kudu maso gabas tsakanin 2021 da 2023, ciki har da Musulmi da Kiristoci.

Post a Comment

Previous Post Next Post